Kotu Ta Tabbatar Rufa'i Da Hanga a Matsayin Zababben Sanatan Kano Ta Tsakiya

Kotu Ta Tabbatar Rufa'i Da Hanga a Matsayin Zababben Sanatan Kano Ta Tsakiya

  • Kotun sauraron ƙararrakin zaɓe mai zamanta a birnin Kano ta yanke hukunci akan ƙarar AA Zaura da Sanata Rufa'i Hanga
  • Kotun ta yi watsi da ƙarar da AA Zaura ya shigar inda ta tabbatar da Hanga a matsayin zaɓaɓɓen sanatan Kano ta tsakiya
  • AA Zaura dai ya shigar da ƙara a gaban kotun yana neman a bayyana shi matsayin wanda ya lashe zaɓen

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kano - Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen ƴan majalisa mai zamanta a Kano ta tabbatar da nasarar Sanata Rufa'i Hanga a matsayin zaɓaɓɓen Sanatan Kano ta tsakiya, rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar.

Ɗan takarar jam'iyyar APC a zaɓen na ranar 25 ga watan Fabrairu, Abdulsalam Abdulkarim Zaura, ya shigar da ƙara a gaban kotun yana ƙalubalantar bayyana Hanga na jam'iyyar NNPP a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen da hukumar INEC ta yi.

Kara karanta wannan

Yanzu: "Duniya Ba Za Ta 'Tashi' Ba Idan Aka Cire Ka Daga Shugaban Kasa", Atiku Ya Mayarwa Tinubu Martani

Kotu ta tabbatar da nasarar Sanata Rufa'i Hanga
Kotu ta yi watsi da karar AA Zaura kan nasarar Sanata Rufai Hanga Hoto: Aminci Radio
Asali: Facebook

Zaura, ta hannun lauyansa Ishaka Dikko (SAN), ya buƙaci kotun da ta bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen sannan ta kawar da bayyana Hanga a matsayin wanda ya lashe zaɓen da hukumar INEC ta yi.

Ya yi zargin cewa zaɓen na kujerar Sanatan Kano ta Tsakiya cike yake da kura-kurai, maguɗi da rashin bin ƙa'idar sabuwar dokar zaɓe.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sai dai, a martaninsu kan shari'ar, waɗanda ake ƙarar su huɗu, hukumar INEC, jam'iyyar NNPP, Hanga, da Ibrahim Shekarau sun haƙiƙance cewa an gudanar da zaɓen bisa bin tanadin doka.

Kotu ta yi watsi da ƙarar AA Zaura kan nasarar Sanata Rufa'i Hanga

Da take gabatar da hukuncinta kan ƙarar a ranar Litinin, 24 ga watan Yuli, kotun mai alƙalai uku ƙarƙashin jagorancin mai shari'a I.P Chima ya bayyana cewa mai ƙarar ya kasa kawo ƙwararan hujjoji a gabanta, cewar rahoton New Telegraph.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar AA Ta Taso Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai a Gaba, Tana Neman Kwace Kujerarsa

"Wanda ya shigar da ƙarar ya kasa tabbatar da rashin bin tanadin sabuwar dokar zaɓe ta shekarar 2022, a don haka mun yi watsi da wannan ƙarar.
"Haka kuma wanda ya shigar da ƙarar zai biya wanda ake ƙara na biyu NNPP tsabar kuɗi har N3000,000 kuɗin wahalar da ta sha, sannan zai biya wanda ake ƙara na ɗaya, na biyu, na uku da na huɗu tsabar kuɗi har N300,000."

Abba Gida-Gida Ya Rufe Shari'arsa Da Shaida 1

A wani labarin kuma, gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya rufe shari'arsa da sakataren gwamnatin jihar a matsayin shaidarsa shi kaɗai.

Jam'iyyar APC ta maka gwamnan ƙara a gaban kotu inda take ƙalubalantar nasarar da ya samu a zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar, ranar 18 ga watan Maris.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel