“Sama Ba Za Ta Faɗo Ba Idan Aka Cire Ka Daga Matsayin Shugaban Kasa,” Atiku Ya Fadawa Tinubu

“Sama Ba Za Ta Faɗo Ba Idan Aka Cire Ka Daga Matsayin Shugaban Kasa,” Atiku Ya Fadawa Tinubu

  • Dan takarar shugabancin ƙasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya nemi kotu ta soke nasarar Tinubu
  • Atiku ya ce sama ba za ta faɗo ba don kotun sauraron ƙararrakin zaɓen ta soke zaɓen Shugaba Tinubu
  • Ya kuma yi kira da kotun ta yi ƙoƙarin yanke hukunci cikin adalci ba tare da jin tsoron duk wata barazana ba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Dan takarar shugabancin ƙasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya nemi kotun sauraron ƙararrakin zaɓe da ta tsige shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu daga kujerarsa.

Atiku a wani saƙo da ya aikowa Legit.ng ya shaidawa Tinubu da jam'iyyarsa ta APC cewa sama ba za ta faɗo ba idan kotu ta tsige Tinubu daga kujerarsa.

Atiku ya nemi kotu ta tsige Tinubu daga kujerarsa
Atiku ya nemi kotu ta rungume Shugaba Tinubu, ya ce sama ba za ta faɗo ba. Hoto: Atiku Abubakar, Ahmed Bola Tinubu
Asali: Twitter

Atiku ya roƙi kotun ta yi ta maza wajen tsige Tinubu

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Kotu Ta Tabbatar Da Sahihin Wanda Ya Lashe Zaben Sanatan Kano Ta Tsakiya

Atiku ya roƙi kotun sauraron ƙararrakin zaɓen da ta yi ta maza, wajen cika roƙon da ya yi, na neman soke nasarar da Tinubu ya yi a zaɓen da ya gabata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wani rahoto da jaridar Vanguard ta wallafa, Atiku ya ce ba hujja ba ce kotun ta ƙi soke nasarar Tinubu don kawai ba a taɓa yin irin hakan a baya ba.

Atiku ya kuma yi kira ga kotun sauraron ƙararrakin zaɓen, da kada barazana ko wani zare idanu su hana ta yanke hukunci bisa adalci.

Ya nemi kotun da ta yanke hukunci yadda yake ko menene zai faru ya faru.

Atiku ya zargi hukumar zaɓe da gaza bayar da sahihin sakamakon zaɓe

Alhaji Atiku Abubakar, ya kuma zargi hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), kan gaza bayar da sahihin sakamakon zaɓe.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar AA Ta Taso Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai a Gaba, Tana Neman Kwace Kujerarsa

Ya bayyana cewa shaidar da hukumar ta gabatar a gaban kotu, ya tabbatar da cewa hukumar ba ta tafiyar da zaɓen yadda ya kamata ba.

Atiku ya kuma ƙara da cewa na'urar da aka samar da zummar ta riƙa aikawa da sakamakon zaɓen kai tsaye zuwa shafin hukumar domin tabbatar da sahihanci, ba a yi aiki da ita yadda ya kamata. ba.

Ya dogara da cewa, shaidar ya bayyana cewa a lokacin da aka sanar da sakamakon zaɓen, ba a gama ɗora shi akan shafin hukumar ba.

Tinubu ya nemi a soke sammacin da Atiku ya yanko masa a kotun Amurka

Legit.ng a baya ta kawo rahoto inda Shugaba Tinubu ya nemi kotu ta soke wani sammaci da Atiku ya yanko masa a wata kotu da ke ƙasar Amurka.

A cikin sammacin, Atiku ya nemi Tinubu ya gurfana a gaban kotun da ke Illinois na ƙasar Amurka domin bayarda bayanai kan karatunsa.

Kara karanta wannan

Labari Mai Daɗi: Shugaba Tinubu Ya Sake Magana Mai Jan Hankali Kan Matsalar Tsaron Najeriya

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng