Abba Gida Gida Ya Kawo Tsaiko a Zaman Sauraron Karar Zaben Gwamnan Kano

Abba Gida Gida Ya Kawo Tsaiko a Zaman Sauraron Karar Zaben Gwamnan Kano

  • A zaman sauraron ƙarar zaben gwamnan jihar Kano ranar Jumu'a, gwamna Abba Kabir Yusuf ya kawo cikas
  • Rashin halartar shaidu 3 da gwamnan ya shirya gabatarwa ya tsaida zaman har Kotu ta ɗage zuwa 22 ga watan Yuli
  • Tuni dai APC mai shigar da ƙara ta gabatar da shaidu 32 kan zargin da take wa INEC a gaban Kotun zaɓe

Kano state - Rashin halartar shaidun gwamna Abba Kabir Yusuf a zaman ci gaba da sauraron ƙarar zaben gwamnan Kano ya kawo cikas.

Jaridai Daily Trust ta rahoto cewa mai shigar da ƙara watau APC ta kalubalancin hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) bisa ayyana Abba Kabiri Yusuf na jam'iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaɓe.

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar NNPP
Abba Gida Gida Ya Kawo Tsaiko a Zaman Sauraron Karar Zaben Gwamnan Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Idan zaku iya tuna wa gwamna Yusuf, wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida ya samu nasara lashe zaɓen gwamnan Kano wanda ya gudana ranar 18 ga watan Maris, 2023 da ƙuri'u mafi rinjaye.

Kara karanta wannan

Shaidan PDP Ya Dabarbarce a Gaban Kotu, Ya Yi Magana Daga Baya Ya Warwareta

Sai dai APC ta roƙi Kotu ta ayyana cewa jam'iyyar NNPP ba ta da ɗan takarar gwamna saboda ba bu sunan Abba Gida Gida a rijistar halatattun mambobin NNPP da ke hannun INEC a lokacin zaɓen.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

APC ta shigar da karar INEC, Abba Gida Gida da jam'iyyar NNPP a matsayin waɗanda take tuhuma na ɗaya, na biyu da na uku.

Yadda Abba Gida-Gida ya jawo tsaikon a zaman ranar Jumu'a

Yayin ci gaba da zaman sauraron ƙarar ranar Jumu'a, lauyan Abba Gida-Gida, Eyitayo Fatigun (SAN), ya shaida wa Kotu cewa sun tanadi shaidu uku da zasu gabatar.

Lauyan ya ce:

"Mai girma mai shari'a muna bada haƙuri saboda shaidun mu sun samu matsalar jirgin da zasu biyo daga Abuja, muna rokon a ƙara bamu lokaci."

Lauyan INEC, Emmanuel Osayomi (SAN) da lauyan wanda ake tuhuma na uku NNPP, John Olusola (SAN), ba su yi jayayya da buƙatar ƙara ɗage zaman ba.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Manyan Shugabannin APC Na Ƙasa Zasu Sa Labule da Gwamnoni a Abuja, Bayanai Sun Fito

Kwamitin alkalai uku karkashin jagorancin mai shari'a Oluyemi Akintan Osadebay, ya karɓi uzurin kana ya ɗage zaman zuwa ranar 22 ga watan Yuli, 2023 domin sauraron shaidun gwamna.

Idan zaku iya tuna wa APC ta gabatar da shaidu 32 a gaban Kotun yayin da INEC ta gaza gabatar da shaida ko ɗaya, kamar yadda Guardian ta rahoto.

Jerin Sunayen Gwamnonin da Ba Su Fara Biyan Mafi Karancin Albashin N30,000 Ba Ya Bayyana

A wani labarin na daban kuma Mun kawo muku jerin sunayen jihohi 16 da NULGE ke zargin har yanzu ba su aiwatar da mafi ƙarancin albashin N30,000 ba.

Ƙungiyar ta nuna takaicinta musamman yadda har yau jihar Zamfara ba ta aiwatar da tsohon mafi karancin albashi N18,000 ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262