An Gano Tinubu Na Alkawarin Rage Farashin Mai Idan Ya Hau Mulki Yayin Yakin Neman Zabe, Bidiyon Ya Yadu
- Yayin yakin neman zaben shugabancin kasar nan, Bola Tinubu ya bayyana cewa zai rage farashin man fetur
- A wani faifan bidiyo, an gano Tinubu na sukar tsohuwar gwamnati da gazawa wurin gudanar da albarkatun mai
- Ya bayyana haka ne a birnin Abeokuta na jihar Ogun inda ya yi magana da harshen Yarbanci
Jihar Ogun - Wani faifan bidiyo ya tuno wa 'yan abin da ke damunsu bayan ganin Bola Tinubu na cewa idan ya samu mulki zai rage kudin litar mai.
Yayin yakin neman zabe a Abeokuta ta jihar Ogun a ranar 25 ga watan Janairu, an jiyo Tinubu na alkawarin rage farashin litar mai da zarar ya hau mulki, Legit.ng ta tattaro.
Tinubu ya bayyana haka da harshen Yarbanci ganin mafi yawan jama'an da ke wurin Yarbawa ne inda ya ce mulkinsa zai zo wa mutane da sauki.
Ya yi alkawarin rage farashin da zarar ya hau mulki
Ya ce duk da mutane sun yarda farashin zai iya kai N200, amma za a duba a kai kuma zai ragu idan suka hau mulki, Daily Trust ta ruwaito.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewarsa:
"Masu girma matasan Najeriya, masu girma daliban Najeriya, wannan juyin juya hali ne, wannan zabe juyin juya halin ne.
"Suna kokarin kawo cikas, amma za su fadi, sun ce litar mai za ta kai N200 zuwa N500, kada ku ji komai za mu karya farashi.
"Ba sa son a yi wannan zaben, suna son kawo cikas a zaben, za ku bar su?.
Tinubu ya yi tambaya ga magoya bayansa da ke wurin inda suka amsa da cewa a'a, cewar Punch.
Tinubu ya ce ko babu fetur sai sun je zabe
Tinubu ya ce ko babu fetur za su taka da kafa don gudanar da zabe a Najeriya.
Ya kara da cewa:
"Ko sun ce babu mai sai mun taka da kafa munje yin zabe, suna da mugunta, za su iya cewa babu mai, suna neman yadda za su yi don kawo karancin mai."
Shehu Sani Ya Fadi Abin Da Mutane Za Su Yi Kafin Karbar Tallafin Tinubu
A wani labarin, sanatan Kaduna ta tsakiya ya soki shirin ba da talllafi na Shugaba Bola Tinubu bayan cire tallafin mai.
Shugaba Tinubu ya ware N500bn don rabawa gidaje miliyan 12 har N8,000 na tsawon watanni shida.
Sani ya kushe tsarin inda ya ce babu abin da za su rage sai kara talauci, ya ce mutum ya yi addu'a kafin karba.
Asali: Legit.ng