Cire tallafi: 'Yan Najeriya Ba Su Tsammaci Shan Irin Bakar Wahalar Nan Ba, Gani Adams Ya Caccaki Tinubu
- Basarake kuma mai fada a ji a jihohin Yarabawa, Cif Gani Adams ya caccaki salon mulkin shugaba Tinubu
- Ya ce Najeriya ce kadai kasa mai arzikin man fetur da 'yan kasar ke shan wahala saboda tsadar man a duk duniya
- Ya nemi shugaba Tinubu da ya yi kokarin nemo hanyoyin da zai shawo kan matsalar tsadar rayuwa da ake fama da ita
Mai fada a ji kuma basarake a kasar Yarabawa, Cif Gani Adams, ya nuna rashin jin dadinsa dangane da salon mulkin Shugaba Tinubu, musamman ma cire tallafin man da ya jefa 'yan kasa cikin halin kunci.
Ya bayyana hakan ne ranar Alhamis, ta hannun mai taimaka masa a kafafen yada labarai, Kehinde Aderemi kamar yadda The Punch ta wallafa.
Najeriya ce kadai mai arzikin man da takawanta ke sha wahala a duniya
Adams ya ce 'yan Najeriya ba su yi tsammanin za su sha irin wannan wahalar ba a karkashin mulkin Bola Tinubu.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya kara da cewa a duk duniya Najeriya ce kadai kasa mar arzikin man fetur da 'yan kasarta ke shan wahala saboda tsadar man.
Adams ya kuma koka kan yadda farashin man fetur ya tashi daga naira 187 a duk lita zuwa 500, sannan ya carke zuwa 617 cikin watanni biyu, duk a dalilin abinda ya kira da cire tallafi na rashin lissafi.
Adams ya shawarci Tinubu da ya yi kokarin nemo mafita
Gani Adams ya bayyana cewa babu wata gwamnati da za ta rika jin dadi a lokacin da 'yan kasa ke shan bakar ukuba.
Ya kara da cewa ba abinda sukai tsammani daga Shugaba Tinubu ba kenan, musamman ma da ya zamto ya fito ne daga yankin Kudu maso Yamma kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Adams ya shawarci Tinubu da ya yi kokarin magance wannan matsala ta tsadar rayuwa da ake fama da ita a Najeriya.
Ya ce shugabannin kasashen duniya da dama sun sanya tallafi cikin kayayyakin da talakawansu ke amfani da su domin saukaka musu rayuwa.
Tinubu na neman kare kansa kan sammacin da Atiku ya yanko masa a Amurka
Legit.ng a baya ta kawo muku wani rahoto da ke cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya nemi a soke wani sammaci da Atiku Abubakar ya yanko masa a wata kotu da ke Amurka.
Atiku a cikin sammacin, yana neman sanin sahihancin bayanan karatun Shugaba Tinubu.
Asali: Legit.ng