Ganduje, Almakura Na Fafatawa Don Ganin Sun Dare Kujerar Shugabancin jam'iyyar APC
- Shugabancin jam'iyyar APC ta dauki sabon salo kan wanda zai gaji kujerar jam'iyyar tun bayan murabus da Sanata Abdullahi Adamu ya yi
- A yanzu haka, tsoffin gwamnoni biyu ne ke dakon kujerar shugabancin jam'iyyar da ake ganin na iya jefa jam'iyyar cikin matsala
- Tsoffin gwamnonin sun hada da na jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje da kuma takwaransa Tanko Almakura na jihar Nasarawa
FCT, Abuja - Fafatawar neman kujerar shugabancin jam'iyyar APC ta dawo tsakanin tsoffin gwamnoni gida biyu.
Tsoffin gwamnonin sune Abdullahi Umar Ganduje na Kano da kuma Tanko Almakura na jihar Nasarawa.
Vanguard ta tattaro cewa masu ruwa da tsaki daga yankin Arewa ta Tsakiya sun shiga fafatawar don ganin dansu ya samu.
Yadda jiga-jigan jam'iyyar APC suka ki Ganduje kan shugabancin jam'iyyar
Amma akwai yiyuwar Shugaba Bola Tinubu na iya mika shugabancin jam'iyyar ga tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Jiga-jigan jam'iyyar ba sa goyon bayan shugabancin Ganduje ganin yadda yankin da ya fito ta samu kakakin majalisa da kuma mataimakin shugaban majalisar Dattawa.
Tun farko a sakatariyar jam'iyyar, ana sa ran Tanko ne zai zama shugaban jam'iyyar kafin daga bisani labarin ya sauya, Concise ta tattaro.
Babu sunan Ganduje a cikin jerin ministoci
Ana sa ran za a cire sunan Ganduje a cikin jerin sunayen ministoci don maye gurbin shugaban jam'iyyar da ya yi murabus, cewar Leadership.
Wata majiya daga jam'iyyar ta tabbatar da cewa:
"Shugaba Tinubu ya yanke shawarar zaban Ganduje a matsayin shugaban jam'iyyar APC.
"Tinubu ya riga ya saka sunan Ganduje a matsayin minista, amma saboda yadda ya ke da kwarin guiwa akansa ya sauya masa zuwa shugancin jam'iyya.
Tinubu Ya Yarda Ganduje Ya Zama Sabon Shugaban APC
A wani labarin, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da ya nada tsohon gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje a matsayin shugaban jam'iyyar APC.
Idan ba a mantaba, tsohon shugaban jam'iyyar APC, Sanata Abdullahi Adamu ya yi murabus a ranar Litinin 17 ga watan Yuli bisa zargin cewa magoya bayan Shugaba sun sa shi a gaba.
Hakan na cikin matsayar da aka fara neman a cin ma a wata ganawa da aka yi tsakanin shugaban kasa, Bola Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima da kuma wasu Gwamnonin APC.
Asali: Legit.ng