Shaidan PDP Ya Dabarbarce a Gaban Kotu, Ya Yi Wa Kotu Magana Biyu
- Shaidan ɗan takarar gwamnan PDP a kotun sauraron ƙarar zaɓen gwamnan jihar Kaduna, Steven Luka Bivan, ya yi magana biyu a gaban kotun
- Steven Luka-Bivan, ya yi iƙirarin shi injiniyan manhajar na'ura mai ƙwaƙwalwa ne amma ya ce bai taɓa amfani da na'urar BVAS ba lokacin da ake masa tambayoyi
- Luka-Bivan ya yi iƙirarin cewa baya daga cikin tawagar da suka samar da BVAS amma ya ce ya yi magana ne kawai kan yanayin aikinta lokacin da ya yi rantsuwa
Kaduna, Kaduna - An samu dirama a kotun sauraron ƙarar zaɓen gwamnan jihar Kaduna a ranar Laraba, 19 ga watan Yuli, lokacin da shaidan jam'iyyar PDP da ɗan takararta, Isah Mohammed Ashiru Kudan, Steven Luka Bivan, ya yi magana biyu a gaban kotun.
Jaridar Nigerian Tribune ta rahoto cewa jam'iyyar PDP da ɗan takararta sun gabatar da injiniyan manhajar na'ura mai ƙwaƙwalwa, Steven Luka-Bivan, domin bayar da shaida kan ƙarar da suka shigar.
Yadda taƙaddamar ta kaya a kotun sauraron ƙarar zaɓen gwamnan jihar Kaduna
Sai dai, Luka-Bivan, bayan ya yi iƙirarin cewa ya san na'uarar BVAS, ya warware kalamansa lokacin da lauyoyin waɗanda ake ƙara suka yi masa tambayoyi, inda ya ce bai taɓa amfani da na'urar BVAS ba.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Bayan ya yi iƙirarin cewa baya daga cikin tawagar da suka samar da BVAS, daga baya ya zo ya ce magana kawai ya yi akan yadda na'uarar ta ke aiki a rantsuwar da ya yi, rahoton The Sun ya tabbatar.
Hukumar zaɓe ta ƙasa mai zaman kanta (INEC) ta bayyana ɗan takarar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a zaɓen gwamnan jihar na ranar 18 ga watan Maris, a matsayin wanda ya yi nasarar lashe zaɓen.
Jam'iyyar PDP da ɗan takararta sun yi zargin an tafka maguɗi a zaɓen inda suka garzaya kotu domin ƙalubalantar sakamakon zaɓen.
A yayin da ake ci gaba da sauraron ƙarar, an rantsar da wanda ya yi nasara a zaɓen, Malam Uba Sani, a matsayin gwamnan jihar bayan ƙarewar wa'adin mulkin tsohon gwamna, Nasir El-Rufai a ranar 29 ga watan Mayu.
Shaidan PDP Ya Rikice a Gaban Kotu
A wani labarin kuma, shaidan da jam'iyyar PDP ta gabatar a gaban kotun sauraron ƙarar zaɓen gwamnan jihar Ogun, ya kunyata jam'iyyar a gaban kotu.
Shaidan ya kasa tabbatar da cewa shi wakilan akwatu ne bayan jam'iyyar ta gabatar da shi a matsayin ɗaya daga cikin shaiɗunta.
Asali: Legit.ng