Tsohon Gwamna Ya Rasa, Tinubu Ya Yarda Ganduje Ya Zama Sabon Shugaban APC

Tsohon Gwamna Ya Rasa, Tinubu Ya Yarda Ganduje Ya Zama Sabon Shugaban APC

  • Abdullahi Umar Ganduje ya kama hanyar zama sabon shugaban jam’iyyar bayan Abdullahi Adamu
  • Da farko ana tunanin tsohon Gwamnan Kano yana cikin sunayen wadanda za a ba kujerar Minista
  • Tsakanin Gboyega Oyetola da Ajibola Basiru za a samu wanda zai zama sabon sakataren APC

Abuja – Idan dai ba abubuwa sun sauya zani ba, tsohon Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ne zai zama sabon shugaban jam’iyyar APC.

A rahoton da aka samu daga This Day, an fahimci su Bola Ahmed Tinubu sun yarda Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya jagoranci jam’iyya mai-mulki.

Wannan ya na cikin matsayar da aka fara neman a cin ma a zaman da shugaban kasa da Kashim Shettima su ka yi da wasu Gwamnonin APC.

Shugaban APC Ganduje
Tinubu, Ganduje a cikin manyan APC da Gwamnati Hoto: Abubakar Aminu Ibrahim
Asali: Facebook

Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya halarci taron bayan an yada cewa za a sanar da sunayen wadanda za su zama Ministocin tarayya.

Kara karanta wannan

Wanda Ya San Ciki da Wajen APC, Ya Haska Kuskuren Tsohon Shugaban Jam’iyya 3

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ganduje a taron PGF

Da jin shugaban jam’iyya da sakatarensa sun yi ritaya, aka ji labari gwamnonin APC a karkashin jagorancin Hope Uzodinma su ka kira zama a Abuja.

Wata majiya ta ce a taron da aka yi, an ga Abdullahi Ganduje, hakan ya nuna shi ake so ya canji Abdullahi Adamu da ya yi murabus daga kujerar APC.

Sanata Jibrin Barau ya kawo Ganduje zuwa wajen taron, bayan shugaban kasa ya nuna masa zai rike jam’iyya a maimakon Minista da aka niyyar ba shi.

Kujerar Sakataren APC

Duk da ba a san wa jam’iyyar take so ya maye gurbin Sanata Iyiola Omisore ba, amma an fara kishin-kishin cewa za a ba Gboyega Oyetola mukamin.

A wani kaulin kuma, sunan Sanata Ajibola Basiru ake yawo da shi a matsayin sabon Sakataren jam’iyyar APC, dukkansu daga jihar Osun su ka fito.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Bukaci Majalisa ta nada Mutanen da Buhari Ya Ki Amincewa da su a Gwamnati

Ganduje ya doke Tanko Al-Makura?

A halin da ake ciki, bangaren CPC da ke tare da Muhammadu Buhari ba za su samu wannan kujera ba, Leadership ta ce an sha gaban Tanko Al-Makura.

Sanata Al-Makura yana cikin wadanda ake tunani za su iya samun shugabancin APC na kasa, musamman ganin shi ma tsohon Gwamnan Nasarawa ne.

Wa zai jagoranci jam'iyyar APC?

A baya kun ji rahoto cewa watakila daga Arewa ta tsakiya a samu wanda zai karbi kujerar Abdullahi Adamu wanda ya yi murabus a makon jiya.

Na-hannun daman Bola Tinubu¸ Hon. James Faleke da tsohon Gwamnan Filato, Simon Lalong su na cikin wadanda ake ganin su na harin kujerar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng