Majalisar Wakilai Ta Tabbatar Da Nadin Hafsoshin Tsaro Bayan Tantancesu

Majalisar Wakilai Ta Tabbatar Da Nadin Hafsoshin Tsaro Bayan Tantancesu

  • Majalisar Wakilai a Najeriya ta tabbatar da nadin hafsoshin tsaron kasar bayan kammala tantance su
  • A ranar Litinin 17 ga watan Yuli ne majalisar ta fara tantance hafsoshin tsaron a dakin majalisar da ke Abuja
  • Shugaba Tinubu ya nada sabbin hafsoshin tsaron a ranar 19 ga watan Yuni don kawo sauyi a shugabancin tsaro a kasar

FCT, Abuja - Majalisar Wakilai a Najeriya ta tabbatar da nadin sabbin hafsoshin tsaro bayan kammala tantance su a ranar Litinin 17 ga watan Yuli.

Wadanda aka tantance din sun hada da hafsan sojin kasa, Manjo Janar Taoreed Lagbaja da hafsan tsaro na kasa, Manjo Janar Chistopher Musa.

Majalisar Wakilai Ta Tabbatar Da Nadin Hafsoshin Tsaro Da Tinubu Ya Bukata Bayan Kammala Tantancesu
Majalisar Wakilai A Najeriya Ta Kammala Tantance Sabbin Hafsoshin Tsaro Tare Da Tabbatar Da Nadinsu. Hoto: Channels TV.
Asali: Facebook

Sauran sun hada da hafsan sojin sama, Hassan Bala Abubakar da hafsan sojin ruwa, Emmanuel Ikechukwu Ogalla, cewar Channels TV.

Majalisar ta fara tantance hafsoshin tsaron a ranar Litinin

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Farmaki Har Cikin Fada, Sun Halaka Babban Sarki a Najeriya

Tabbatar da nadin ya biyo bayan amincewar kwamitin wucin gadi na majalisar da ta tantance hafsoshin tsaron.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisar Wakilai ta fara tantance hafsoshin tsaron a ranar Litinin 17 ga watan Yuli kwanaki kadan bayan majalisar Dattawa ta gama tabbatar da nadinsu.

Shugaban masu rinjaye na majalisar, Julius Ihonvbere shi ya jagoranci kwamitin tantancewar.

Tinubu ya nada sabbin hafsoshin tsaron tun a watan Yuni

Shugaban kwamitin wucin gadin, Babajimi Benson ya ce dole hafsoshin tsaron su bi dokokin kasa, The Guardian ta tattaro.

Ya kara da cewa akwai bukatar sanar da junansu wasu bayanan sirri da za su taimaka wurin kawo karshen rashin tsaro a kasar.

Ya ce majalisar za ta sake duba akan nadin nasu idan hafsoshin sun gudanar da gudanar da ayyukansu yadda ya dace bayan tabbatar da su.

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya nada sabbin hafsoshin tsaron a ranar 19 ga watan Yuni makwanni uku dai-dai bayan hawanshi karagar mulki.

Kara karanta wannan

Farin Ciki: Sojoji Sun Kama Wasu 'Yan Kasar Waje Da Ke Kokarin Shigo Da Muggan Makamai Cikin Najeriya Maƙare A Mota

Majalisar Wakilai Ta Shiga Aikin Tantance Sabbin Hafsoshin Tsaro Da Tinubu Ya Mika Musu

A wani labarin, a ranar 17 ga watan Yuli ne 'yan majalisar Wakilai suka fara tantance sabbin hafsoshin tsaro da Shugaba Tinubu ya tura majalisar.

Shugaban kasa, Bola Tinubu ya nada sabbin hafsoshin tsaron ne a ranar 19 ga watan Yuni don inganta tsaron kasar.

Hawan shugaban kasa, Bola Tinubu ke da wuya ya rusa dukkan tsoffin hafsoshin tsaron kasar tare da nada nashi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.