Yanzu: Gwamnatin Katsina Ta Bayyana Sunayen Kwamishinonin Jihar Guda 20
- Gwamnan Katsina, Dikko Umar Radda, ya aika da sunayen mutanen da yake son naɗawa kwamishinoni zuwa Majalisar Dokokin jihar
- Shugaban masu rinjaye na Majalisar, Shamsuddeen Abubakar Dabai ne ya karanto sunayen mutane ashirin da Dikko yake son yin aiki tare da su matsayin kwamishinoni
- Majalisar ta tsaida ranar Litinin 24, da ranar Talata 25 ga watan Yuli a matsayin ranar da za ta tantance sabbin kwamishinonin
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Katsina - Majalisar Dokokin jihar Katsina ta bayyana sunayen kwamishinoni 20 da gwamna Dikko Radda ya aika mata domin tantancesu.
Majalisar ta bayyana sunayen kwamishinonin ne a zaman da ta gabatar ranar Laraba, 19 ga watan Yulin 2023 kamar yadda daraktan yaɗa labarai a kafafen sadarwa na gwamnatin jihar, Maiwada Dammalam ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Shugaban masu rinjaye na majalisar, Honarabul Shamsuddeen Abubakar Dabai ne ya bayyana sunayen kwamishinonin dake ƙunshe a cikin wata takarda da gwamnan ya aike zuwa majalisar.
Sunayen Kwamishinonin jihar Katsina 20 da aka bayyana:
(1) Farfesa Ahmed Muhammad Bakori, daga karamar hukumar Bakori.
(2) Ishaq Shehu Dabai daga karamar hukumar Danja
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
(3) Farfesa Badamasi Lawal Charanci daga karamar hukumar Charanci.
(4) Dakta Nasiru Mu'azu Danmusa daga karamar hukumar Danmusa
(5) Malam Bala M. Salisu daga karamar hukumar Zango .
(6) Farfesa Abdul Hamid Ahmed daga karamar hukumar Mani.
(7) Honarabul Musa Adamu Funtua daga karamar hukumar Funtua.
(8) Alhaji Yusuf Rabi'u Jirdede daga karamar hukumar Mai'adua
(9) Honarabul Aliyu Lawal Zakari daga karamar hukumar Dutsi.
(10) Honarabul Bishir Tanimu Gambo daga karamar hukumar Dutsinma.
(11) Honarabul Hamza Suleiman Faskari daga karamar hukumar Faskari.
(12) Alhaji isa Muhammad Musa daga karamar hukumar Kankara.
(13) Injiniya Dakta Sani Magaji Ingawa daga karamar hukumar Ingawa.
(14) Dakta Faisal Umar Kaita daga karamar hukumar Kaita.
(15) Alhaji Bello Husaini Kagara daga karamar hukumar Kafur.
(15) Hajiya Hadiza Yaradua daga karamar hukumar Katsina.
(17) Hajiya Zainab M. Musawa daga karamar hukumar Musawa.
(18) Alhaji Musa Na Habu daga karamar hukumar Daura.
(19) Dakta Bishir Gambo Saulawa daga karamar hukumar Katsina.
(20) Barista Fadila Muhammad Dikko daga karamar hukumar Kurfi.
Bayan karanta sunayen, majalisar ta tsaida ranar Litinin 24, da ranar Talata 25 ga watan Yuli, a matsayin ranakun da za ta tantance wadanda za a naɗa mukamin kwamishinonin.
Dikko Radda ya gana da tsohon gwamnan jihar Katsina Ibrahim Shema
A baya Legit.ng ta kawo rahoto cewa gwamnan jihar Katsina mai ci, Dikko Umar Radda ya gana da tsohon gwamnan jihar, Barista Ibrahim Shehu Shema a gidan gwamnatin jihar.
Shema da 'yan tawagarsa sun ziyarci gwamnan ne a ranar Talata, 18 ga watan Yuli, inda suka tattauna batutuwa masu muhimmanci.
Shema ya kuma taya Radda murnar rantsar da shi da aka yi a matsayin gwamnan jihar Katsina.
Buhari ya ziyarci Dahiru Mangal kan rasuwar matarsa
Legit.ng a baya ta kawo muku rahoto cewa, tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya ziyarci attajirin nan Dahiru Barau Mangal, domin yi masa ta'aziyya bisa rasuwar matarsa.
Haka nan Buhari tare da rakiyar gwamnan jihar, sun ziyarci fadar mai martaba sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman.
Asali: Legit.ng