Labari Mai Zafi: Buhari Yana Halartar Taron Farko Bayan Sauka Daga Shugaban Kasa

Labari Mai Zafi: Buhari Yana Halartar Taron Farko Bayan Sauka Daga Shugaban Kasa

  • Muhammadu Buhari yana cikin masu halartar taron Gidauniyar jihar Katsina na wannan shekarar.
  • Dikko Radda ya yi Muhammadu Buhari lale maraba da zuwa taron da za ayi a gidan Gwamnati.
  • An hangi Farouk Lawal Jobe tare da Mai girma Gwamna yayin da tsohon shugaban kasar ya iso.

Katsina - Mai girma Dikko Umaru Radda, shi ne ya tarbo Muhammadu Buhari zuwa wani taron gidauniyar jihar Katsina a yau.

A yau Laraba za a fara wannan babban taro, kuma kamar yadda bidiyoyi su ka tabbatar, Muhammadu Buhari yana halarta.

Hadimin Gwamnan jihar Katsina, Isa Miqdad, ya shaida cewa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa wajen taron dazu.

Shugaban Kasa Buhari
Muhammadu Buhari da Aisha Buhari Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Bidiyo ya fito yanzu

Isa Miqdad mai taimakawa Gwamna Dikko Umaru Radda wajen harkokin sadarwa na zamani ya wallafa bidiyon a shafin Twitter.

Kara karanta wannan

Masu ba Gwamnan Kano Shawara Sun Doshi 50 Bayan Nade-Naden Sababbin Mukamai

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Za a iya hango mataimakin Gwamnan Katsina, Farouk Lawal Jobe da manyan jami’an gwamnati.

"Da safiyar nan Gwamna Dikko Umaru Radda ya karbi bakuncin tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a gidan gwamnatin Katsina.
Tsohon shugaban kasar yana Katsina domin halartar babban taron gidauniyar jihar Katsina na shekarar nan.
Kuma an yi dace, shi (Buhari) ne shugaban farko da ya rike Gidauniyar Jihar Katsina bayan an kafa ta a tarihi."

- Gwamnatin Katsina

Kwamishinonin jihar Katsina

Sannan kuma a yau shugaban majalisar dokoki, Rt. Hon. Nasir Yahya zai karato wadanda aka zaba a matsayin Kwamishinoni.

Matashin ya shaida hakan a daren yau, bayan an nada karin wasu hadimai da kuma shugabannin hukumomin gwamnati da ke jihar.

Buhari ya je taron farko

Bashir Ahmaad ya tabbatar da wannan zance a Twitter, ya ce tun da Buhari ya mika mulki, wannan ne karon farko da zai je wani taro.

Kara karanta wannan

Yanzu nan: Shugaban APC Ya Hakura da Rikon Jam’iyya, Ya Sauka Daga Kujerarsa

Rahoton da mu ka samu dazu shi ne Gwamnatocin tarayya, jihohi da kananan hukumomi sun tara N1.95tr da za a raba a watan Yulin nan.

Kusan ba a taba samun lokacin da aka samu irin wadannan kudi ba. Cire tallafin fetur ya sa asusun na FAAC ya cika sosai a wannan karo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng