Bayan Dogon Jira Kan Jerin Sunayen Ministoci, Majalisa Za Ta Bayyana Sunayen Ministocin Tinubu a Yau Laraba

Bayan Dogon Jira Kan Jerin Sunayen Ministoci, Majalisa Za Ta Bayyana Sunayen Ministocin Tinubu a Yau Laraba

  • Jerin sunayen ministocin Shugaba Tinubu ya sanya ƴan Najeriya zura ido da sauraren ganin jiga-jigan ƴan siyasar da zai ƙunsa
  • Shugaban ƙasar ya miƙa jerin sunayen ministocin ga majalisar tarayya a ranar Talata, inda ake sa ran za a karanto su a zauren majalisar dattawa a yau Laraba
  • Akwai rahotannin da ke cewa sai da aka miƙa jerin sunayen ga hukumomin EFCC da DSS domin duba ko akwai masu wani guntun laifi a tattare da su

FCT, Abuja - A yau ranar Laraba, 19 ga watan Yuli, ake sa ran za a karanto sunayen mutanen da Shugaba Tinubu zai naɗa a matsayin ministoci a zauren majalisar dattawa, bayan an daɗe ana jira, The Guardian ta yi rahoto.

Hakan na zuwa ne saboda shugaban ƙasar ya aike da jerin sunayen ga majalisar dattawa a ranar Talata, 18 ga watan Yuli, inda ake sa ran za a karanto su a zaman majalisar na yau Laraba.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Magana Ta Ƙare, Shugaba Tinubu Zai Mika Sunayen Ministoci Ga Majalisar Tarayya

Majalisa za ta karanto sunayen ministocin Tinubu
A yau za a bayyana sunayen ministocin Shugaba Tinubu Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Rahotanni sun nuna cewa magatakardan majalisar, Magaji Tambuwal ya karɓi wasiƙar shugaban ƙasar mai ɗauke da sunayen ministocin a ranar Talata.

Shugaban ƙasa Tinubu ya miƙa sunayen ministocin ga hukumomin DSS da EFCC domin yin binciken ƙwaƙwaf a kansu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wasu majiyoyi sun yi iƙirarin cewa hakan da shugaban ƙasar ya yi wata hanya ce ta tsame wasu manyan jiga-jigai waɗanda kai tsaye ba za a iya ƙin basu muƙamin minista ba.

Yaushe Shugaba Tinubu zai bayyana jerin sunayen ministocinsa?

Tolu Ogunlesi, tsohon hadimin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya bayyana a Twitter cewa a cikin satin nan za a bayyana sunayen ministocin, inda ya ƙara da cewa wasu za su dara yayin da wasu kuma za su koka idan sunayen sun bayyana.

Shugaban ƙasar dai yana da daga nan zuwa ranar 27 ga watan Yuli domin bayyana ministocinsa saboda sabuwar dokar da ta umarce shi da gwamnoni su gabatar da sunayen ministoci da kwamishinoni zuwa ga majalisa a cikin kwanaki 60 da hawa kan mulki.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali Yayin Da 'Yan Bindiga Suka Halaka Babban Dan Majalisa a Wata Jiha

Tinubu Ya Dakatar Da Tsarin Tallafi

A wani labarin kuma shugaban ƙasa Bola Tinubu ya bayar da umarnin a dakatar da tsarin bayar da tallafin N8,000 ga iyalai 12m da ya fito da shi.

Shugaban ƙasar ya bayar da wannan umarnin ne domin a sake yin duba da nazari kan tsarin biyon bayan sukar shi da aka yi ta yi a ƙasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng