Manyan Dalilai 5 Da Suka Sanya Abdullahi Adamu Yin Murabus Daga Shugabancin Jam'iyyar APC
A ranar Litinin ne tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu ya yanke shawarar yin murabus daga kan kujerarsa.
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Hakan ya biyo bayan shafe tsawon lokaci da aka yi ana zaman doya da manja tsakaninsa da mafi yawa daga sauran jagororin jam’iyyar ta APC.
Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma ne ya shawarci Adamu da ya yi murabus cikin girmamawa daga kan kujerar tasa kamar yadda The Guardian ta wallafa.
Sanata Abubakar Kyari ya karɓi ragamar jam’iyyar a matsayin shugaba na wucin gadi jim kaɗan bayan murabus ɗin Abdullahi adamu.
An bayyana cewa tun bayan zamansa shugaban jam’iyyar a watan Maris na shekarar 2022, Abdullahi Adamu da Bola Tinubu na yi wa juna kallon hadarin kaji.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ana alaƙanta murabus ɗin da Adamun ya yi da wutar da aka hura masa daga cikin jam’iyya saboda rashin kyakkyawar alaƙarsa da Shugaba Bola Tinubu.
Dalilai 5 da suka sanya Abdullahi Adamu yin murabus daga shugabancin jam’iyyar APC
1. Zargin badaƙalar naira biliyan 32
Mambobi da wasu shugabannin jam’iyyar APC sun zargi Abdullahi Adamu da yin rub da ciki kan naira biliyan 32 da jam’iyyar ta tara gabanin zaben 2023.
Sai dai wasu daga cikin ‘yan jam’iyyar sun ce Adamu ya yi wadaƙa da kuɗaɗen wanda bai fi naira biliyan bakwai ba ce kawai ta rage a asusun jam’iyyar.
A yayin da Adamu ya fahimci ana shirin tsige shi, ya kira shugabannin jam’iyyar na jihohi domin neman goyon bayansu a makon da ya gabata.
2. Ba Abdullahi Tinubu ke so ba
A lokacin da ake ƙoƙarin zaɓen sabon shugaban jam’iyyar ta APC, Tinubu ya nuna goyon bayansa ne ga tsohon gwamnan jihar Nasarawa Tanko Al Makura.
Sai dai jagororin jam’iyyar na lokacin, waɗanda suka kasance masu biyayya ga umarnin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, sun nuna goyon bayansu ga Adamu, wanda ta haka ne ma ya yi nasarar zama shugaban jam’iyyar.
3. Adamu ya yaƙi takarar Tinubu
Wasu ‘yan jam’iyyar na ganin cewa Adamu ya yaƙi Tinubu wajen neman tikitin tsayawa takarar shugaban ƙasa na zaɓen 2023.
An jiyo Shugaba Tinubu na ɓaɓatun cewa ana kokarin a yaudareshi wajen hana shi tsayawa takara duk da alkawarin da aka yi a 2015 na cewa shi zai karba bayan Buhari ya kammala wa’adinsa.
A lokacin kakar zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar APC, Abdullahi Adamu ya fito ya bayyanawa duniya cewa Sanata Ahmad Lawan ne ɗan takarar shugaban kasar da Buhari ke goyon baya ba Tinubu ba kamar yadda Vanguard ta wallafa.
Sai dai hakan ya tayar da ƙura, inda sai da tsohon gwamnan jihar Kebbi, kuma shugaban gwamnonin APC na lokacin, Atiku Bagudu ya samu Shugaba Buhari don gamsar da shi kan ya goyi bayan takarar Tinubu.
4. Adamu ya gaza kawo jiharsa a zaɓen 2023
Daga cikin abubuwan da ake ganin sun taka muhimmiyar rawa wajen tilastawa Abdullahi Adamu yin murabus, akwai gazawar da yayi wajen kawo jiharsa wato Nasarawa a zaben shugaban kasa na 2023 da ya gabata.
A lokacin zaɓen na 2023, Abdullahi Adamu ya gaza kawo koda mazabarsa ballantanar kuma jihar baki daya kamar yadda Premium Times ta ruwaito.
Hakan ya sanya Adamun rasa duk wata ragowa ƙima da manyan cikin jam’iyyar ke ganinsa da ita.
5. Adamu ya goyi bayan Yari
A lokacin da ake ta ƙulle-ƙulle kan shugabancin Majalisar Dattawa, jam’iyyar APC ta bayyana Sanata Godswill Akpabio a matsayin wanda ta tsaida.
Sai dai an bayyana cewa Adamu ya goyi bayan tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari Abubakar ta ƙarƙashin ƙasa, wanda hakan bai yi wa sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyyar daɗi ba kamar yadda yake a wani rahoto na The Cable.
Da Dumi-Dumi: Abdullahi Adamu Ya Yi Magana Kan Murabus Dinsa Daga Shugabancin APC, Ya Bayyana Mataki Na Gaba
An jibge jami'an tsaro gidan tsohon shugaban jam'iyyar APC
Legit.ng ta kawo muku rahoto a bayan kan cewa an hangi jami'an tsaro a gidan tsohon shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Adamu.
An bayyana cewa an hangi jami'an tsaron na zarya a gidan nasa da misalin ƙarfe 03:00 na yammacin ranar Talata 18 ga watan Yuli.
Asali: Legit.ng