"Peter Obi Yana Da Dama Har Yanzu": Faston Da Ya Hango Nasarar Tinubu Ya Kara Magana Mai Daukar Hankali
- An shawarci ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party, Peter Obi da ya yi koyi da tsohon Shugaba Goodluck Jonathan ya karɓi kayen da ya sha da zuciya ɗaya
- Fasto Godwin Ikuru wanda ya yi hasashen nasarar Shugaba Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, shi ne ya bayar da wannan shawarar
- Faston ya yi nuni da cewa har yanzu Peter Obi yana da dama a siyasa, inda ya yi nuni da cewa zai iya samun wani babban muƙami a nan gaba
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Shugaban cocin Foundation of Jehovah High Salvation Ministry, Fasto Godwin Ikuru, ya shawarci ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party (LP), Peter Obi da ya janye ƙarar da ya shigar akan Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
Fasto Ikuru, wanda ya yi hasashen cewa Tinubu zai zama shugaban ƙasa shekara biyu da suka gabata, ya bayyana cewa ya hango Obi na yin rashin nasara a kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa.
Ya bayyana hakan ne a yayin wata hira ta musamman da jaridar Daily Independent wacce aka wallafa a ranar Talata, 18 ga watan Yuli.
An buƙaci Peter Obi ya yi koyi da Jonathan
Malamin addinin ya shawarci Obi da ya koyi darasi daga wajen tsohon shugaba Goodluck Jonathan wanda ya taya tsohon Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari murna bayan ya kayar da shi a zaɓe.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A kalamansa:
"Zai iya yin abinda tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya yi, inda ya je Twitter ya taya tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari murna bayan ya zama shugaban ƙasa a shekarar 2015. A wannan lokacin hankula sun tashi, amma Jonathan na yin magana sai hankula suka kwanta."
"Don haka zai fi kyau ga Peter Obi ya yi hakan a yanzu, maimakon sai ya bari ya sha kashi a gaban kotu saboda na hango shi yana yin rashin nasara a ƙarar."
Fasto Ikuru, ya kuma yi nuni da cewa siyasar Peter Obi ba ta zo ƙarshe ba kenan domin har yanzu yana da sauran damar da zai iya yin mulki
"Mutum irin Mr. Peter Obi yana da sauran damarmaki. Bai zago shugaban ƙasa ba har yanzu. Magana kawai yake akan kujerarsa. A wannan lokacin yana da damar da zai iya watsar da shari'ar." A cewarsa.
Peter Obi Ya Yi Magana Kan Sake Tsayawa Takara a 2027
A wani labarin kuma, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, ya yi magana kan rahotannin da ke cewa yana shirin sake tsayawa takarar shugaban ƙasa a shekarar 2027.
Obi ya bayyana cewa rahotannin basu da tushe ballantana makama inda ya bayyana su a matsayin ƙarya tsagwaronta.
Asali: Legit.ng