Shehu Sani Ya Magantu Kan Halin Da Makusantan Buhari Suka Tsinci Kansu A Jam'iyyar APC Karkashin Tinubu

Shehu Sani Ya Magantu Kan Halin Da Makusantan Buhari Suka Tsinci Kansu A Jam'iyyar APC Karkashin Tinubu

  • Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani ya bayyana cewa a yanzu fa na hannun daman Buhari suna jin jiki a jam'iyyar
  • Sani ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter inda ya ce magoya bayan Buhari sun zama marayu a jam'iyyar yanzu
  • Ya ce Shugaba Bola Ahmed a yanzu Tinubu ya na ta kokarin sai ya tumbuke su a jam'iyyar APC karfi da yaji

Jihar Kaduna - Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani ya yi shagube ga 'yan a mutun tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Ya ce duk wadanda suke tare da tsohon shugaban kasar yanzu sun dawo kamar marayu a jam'iyyar APC mai mulkin kasar.

Shehu Sani Ya Bayyana Halin Da Makusantan Buhari Suka Tsinci Kansu A APC Yanzu
Shehu Sani Ya Ce A Yanzu Makusantan Buhari Sun Dawo Marayu A Jam'iyyar APC. Hoto: Legit.ng.
Asali: Twitter

Sani ya ce Tinubu na son tumbuke makusantan Buhari a jam'iyyar

Shehu Sani ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter a ranar Litinin 17 ga watan Yuli.

Kara karanta wannan

Shugaban Kasa Tinubu Ya Dawo Najeriya Yayin da Rikicin APC Ya Yi Kamari

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce Shugaba Tinubu yamna kokarin tunbuke duk wasu na hannun daman tsohon shugaban kasa, Buhari a jam'iyyar APC.

A cewarsa:

"Magoya bayan Buhari na hakika yanzu sun dawo marayu, ana kokarin tumbukesu daga jam'iyyar."

Dalilin murabus din Abdullahi Adamu daga jam'iyyar

Idan ba a mantaba, Sanata Abdullahi Adamu a ranar Lahadi 16 ga watan Yuli ya yi murabus daga kujerarsa ta shugaban jam'iyar APC.

Cewar Legit.ng Hausa, Adamu ya bayyana cewa ya yi murabus ne saboda taron dangi da na hannun daman Shugaba Tinubu suka masa.

Abdullahi Adamu ya zama shugaban jam'iyyar APC ne a watan Maris na 2022 yayin babban taron jam'iyyar na kasa da aka gudanar a birnin Tarayyar kasar, Abuja, cewar Daily Nigerian.

Adamu shi ne zabin tsohon shugaban kasa, Buhari a wancan lokaci wanda hakan ya yi tasiri wurin yin nasararsa na kasancewa shugaban jam'iyyar ta kasa.

Kara karanta wannan

Shehu Sani Ya Lissafa Manyan Dalilai 2 Da Suka Yi Sanadiyar Ficewar Adamu Daga Matsayin Shugaban APC Na Kasa

Abdullahi Adamu Ya Yi Magana Kan Murabus Dinsa, Ya Bayyana Mataki Na Gaba

A wani labarin, tsohon shugaban jam'iyyar APC, Sanata Abdullahi Adamu ya yi magana a kan murabus da ya yi na shugabancin jam'iyyar.

Adamu ya mika takardar murabus din sa ne a ranar Lahadi 16 ga watan Yuli ga fadar shugaban kasa.

Ya ce zai yi magana a kan dalilin daukar wannan mataki da zarar shugaban kasa, Bola Tinubu ya dawo daga Kenya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.