Sunayen ‘Yan Siyasa 4 Sun Fara Fitowa Cikin Wadanda Za Su Karbi Shugabancin APC

Sunayen ‘Yan Siyasa 4 Sun Fara Fitowa Cikin Wadanda Za Su Karbi Shugabancin APC

  • Akwai yiwuwar Bola Ahmed Tinubu da kan shi zai yi ruwa da tsaki wajen kawo sabon shugaban APC
  • Shugaban APC da sakatare na kasa sun ajiye mukamansu bayan tsawon lokaci ana fama da rikici a jam’iyya
  • An fara yawo da sunayen ‘Yan siyasan yankin Arewa maso tsakiya da za su canji Abdullahi Adamu a NWC

Abuja - A sakamakon murabus da shugaban APC da sakatare na kasa su ka yi murabus, an fara neman wadanda za su maye gurabensu a jam’iyya.

Dazu rahoto ya fito daga Vanguard cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kan shi, ya soma tunanin wadanda suka dace su zama sababbbin shugabanni.

Tun bayan da Bola Tinubu ya lashe zaben shugaban kasa, na kusa da shi su ka fara tunanin wanda za a dauko domin ya canji Abdullahi Adamu a APC.

Kara karanta wannan

Mutane Sun ba APC Shawarar Nada Abdullahi Ganduje a Matsayin Shugaban Jam'iyya

Shugabancin APC
Shugaban Jam'iyyar APC na rikon kwarya Hoto: officialapc.ng
Asali: UGC

Sai dai shugaban kasar ya bi abin a hankali, ya zabi ya dare kan mulki kafin ya waiwayi NWC.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kudi ba su iya fita daga asusun APC

Rahoton ya ce an rufe asusun jam’iyyar APC, kuma ana zargin daga fadar shugaban kasa aka bada wannan umarni kafin Sanata Adamu ya bar ofis.

Hana shugabannin jam’iyya mai-ci damar taba akawun ya jawo matsala wajen biyan bashin da ke wuyan APC, musamman bangaren manema labarai.

Wa zai canji Abdullahi Adamu a NWC?

‘Yan jarida sun fara rade-radin cewa sabon shugaban jam’iyya na kasa ba zai wuce Hon. James Faleke ko kuma Sanata Tanko Umaru Almakura ba.

Legit.ng Hausa ta lura daga cikin sunayen da ke yawo har da tsohon mataimakin Gwamnan Nasarawa, Silas Agara da tsohon Gwamna Simon Lalong.

Zunuban Sanata Adamu, Omisore

Kara karanta wannan

Kura-Kurai, Katobara da Cikas 7 da Abdullahi Adamu Ya Samu a Kujerar Shugabancin APC

The Nation ta ce binciken kudi da aka yi ya jawo Abdullahi Adamu da Iyiola Omisore su ka sauka daga kan kujerunsu tun kafin a kai ga wulakanta su.

Ana zargin majalisar NWC a karkashin jagorancin Adamu da rashin tsara kasafin kudi da NEC za ta amince da shi da kuma gudanar da abubuwa shi kadai.

Tsohon shugaban ya ki kafa kwamitoci da za su jagoranci jam’iyya, sannan ya gaza jawo mata da matasa da masu nakasa da gagara sasanta rikicin gida.

Abdullahi Ganduje ya cancanta?

A jiya ne rahoto ya iso mana cewa masu amfani da shafukan sada zumunta sun ayyana wanda ya dace da kujerar APC bayan tafiyar Abdullahi Adamu.

A cewarsu babu wanda ya dace da zama sabon shugaban jam’iyya irin Dr. Abdullahi Ganduje. Dama dai mutumin Kano bai taba jagorantar APC a tarihi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng