An Bayyana Wanda Shugaba Tinubu Ya Fi Son Ya Nada Minista Daga Jihar Ogun
- Ana hasashen shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu zai dauki Wale Edun a matsayin minister daga jihar Ogun
- Edun a kwanakin nan shugaban ya nada shi a matsayin mai ba shi shawara na musamman a kan harkar kudade
- Majiya daga fadar shugaban ta tabbatar cewa Tinubu ya yanke shawarar ce bayan kai ziyara jihar a kwanakin baya
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja – Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu na tunanin nada Wale Edun a matsayin minister daga jihar Ogun, bayan nada shi mai ba shi shawara na musamman a kan harkar kudade a kwanakin nan.
Legit.ng ta tattaro cewa wata majiya a fadar shugaban kasa ta bayyana cewa Tinubu zai dauki Edun a matsayin minister daga jihar.
Akwai rahotanni da suke cewa a cikin ministocin Bola Tinubu za a samu manyan mutane daga jam’iyyu daban-daban na kasar.
Sahwarwari kan su waye shugaban ya kamata ya nada minista
Wasu na ba wa shugaban shawarar ya dauki kwararru don inganta harkar gwamnatinsa yayin da wasu ke cewa kawai ya sakawa ‘yan jam’iyyarsa ta APC.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Punch ta ruwaito cewa Tinubu ya mika sunayen ministocin zuwa hukumomin DSS da kuma EFCC don tantance su.
Majiyar ba ta yi bayanin ko Edun zai kasance a cikin wadanda za a tantance daga hukumomin DSS da EFCC ba saboda zabin shugaban kasa ne shi.
Majiyar ta fadi yadda Tinubu ya mika sunan Edun a mulkin Buhari
Majiyar ta ce:
“Lamarin Edun abu ne da Shugaba Tinubu ya tattauna da sarakunan gargajiya na jihar Ogun yayin ziyarar da ya kai musa makwanni kadan da suka wuce.”
An tabbatar da cewa Wale Edun shi ne zabin Shugaba Tinubu a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, cewar Business Day.
Amma jiga-jigan jam’iyyar APC a lokacin sun ki amincewa da Edun duk da cewa majiyar ba ta bayyana shekarar da abin ya faru ba, 2015 ko kuma 2019.
Gwamnan PDP Mai Karfin Fada A Ji Ya Samu Shiga Jerin Ministocin Tinubu
A wani labarin, an bayyana cewa daya daga cikin tsoffin gwamnonin PDP ya samu shiga cikin jerin ministiocin Tinubu.
Bola Tinubu har ya zuwa yanzu bai tura sunayen ministoci zuwa majalisa ba don tantance su, wanda ake hasashen 'yan adawa da dama za su samu shiga ciki.
A doka shugaban kasa ya na da kwanaki 60 ne kadai don tura sunayen ministoci zuwa majalisa don a tantance su.
Asali: Legit.ng