Kura-Kurai, Katobara da Cikas 7 da Abdullahi Adamu Ya Samu a Kujerar Shugabancin APC
- Murabus da Abdullahi Adamu ya yi ya kawo karshen zamansa shugaban jam’iyyar APC mai-ci
- Duka-duka tsohon Gwamnan na jihar Nasarawa ya yi watanni 15 da ‘yan kwanaki ne yana rike da NWC
- Sanata Adamu ya gamu da wasu matsaloli da su ka yi sanadiyyar gajeren wa’adinsa a jam’iyyar
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Abuja - A wani rahoto da aka samu daga Daily Trust, an kawo jerin matsaloli da kalubalen da Abdullahi Adamu ya fuskanta da yake rike da APC.
1. Rigima da Salihu Lukman
A baya mun kawo rahotanni a kan sabanin Salihu Lukman da Abdullahi Adamu, mataimakin shugaban jam’iyyar ya soki salon mulkin shugabansa.
Lukman ya yi ta rubuta wasikai da su ka bata sunan majalisar APC NWC har abin ya kai Sakataren APC na kasa, Iyiola Omisore ya maida masa martani.
2. Goyon bayan Ahmad Lawan
Daga baya an ji labarin yadda Adamu ya goyi bayan Ahmad Lawan a zaben tsaida gwani na APC, a karshe Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya samu tikiti.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Adamu ya yi kokarin tallata Sanata Lawan a matsayin zabin APC a takarar shugaban kasan 2023.
3. Rashin kokari a zaben bana
A yayin da APC ta lashe zaben shugaban kasa, LP tayi nasara a akwatin Adamu da ke Keffi a jihar Nasarawa, nasarar Peter Obi ta kunyata shugaban na APC.
4. Rikicin cikin gida
Jaridar ta ce APC a karkashin jagorancin Sanata Adamu ba tayi sasanta rikicin cikin gida a jihohi irinsu Legas, Osun, Bayelsa, Ribas da kuma Kano ba.
Wannan lamari ya taimaka wajen kawowa jam’iyya mai mulki cikas a wasu kujeru a zaben bana.
5. Zaben shugabannin majalisa
Bayan an nada sababbin shugabannin majalisa, sai aka ji shugaban APC yana cewa jam’iyya ba ta san da maganar ba, hakan ya jawo matukar abin kunya.
An ji labarin yadda Gwamnonin APC su ka yi ta kokarin su yi wa tafkar hanci bayan kalamansa.
6. Taron Gwamnonin 1999
Ko da Niyi Adebayo ya jagoranci Gwamnonin da suka yi mulki a 1999 zuwa wajen Bola Tinubu, an yi mamaki da ba a ga Adamu wanda yana cikinsu ba.
Sai dai baya ga shugaban na APC, legit.ng Hausa ta lura Rabiu Kwankwaso bai halarci taron ba.
7. Rashin lafiyar Akeredolu
A taron NWC da shugabannin APC na jihohi, Sanata Adamu ya shaidawa Duniya cewa Gwamna Oluwarotimi Akeredolu yana jinya, har bai iya yin komai.
Dole aka ji Sakataren APC da gwamnatin Ondo sun nesanta kansu da kalaman shugaban jam’iyyar.
Shugabanni 5 a shekaru 9
An samu labari rigimar APC za ta dauki salo na dabam yayin da Abdullahi Adamu ya rubuta takardar murabus, ya hakura da shugabancin jam’iyyar.
Abdullahi Adamu zai bi sahun Mai Mala Buni, Adams Oshiomhole, John Oyegun. A yanzu jam’iyyun APC da PDP ba su da cikakkun shugabanni.
Asali: Legit.ng