Yanzu nan: Shugaban APC Ya Hakura da Rikon Jam’iyya, Ya Sauka Daga Kujerarsa

Yanzu nan: Shugaban APC Ya Hakura da Rikon Jam’iyya, Ya Sauka Daga Kujerarsa

  • Abdullahi Adamu ya rubuta takardar murabus, za a samu sabon shugaban da zai jagoranci APC NWC
  • Wani daga cikin ‘yan majalisar NWC ya ce tsohon Sanatan jihar Nasarawa ya ajiye mukaminsa
  • Tun tuni ake samun rashin jituwa tsakanin shugabannin jam’iyyar APC da aka nada a farkon 2022

Abuja - Jita-jita sun zagaye gari daga dare zuwa yanzu cewa Abdullahi Adamu ya yi murabus daga kan kujerarsa ta shugaban jam’iyyar APC.

Daily Trust ta fitar da rahoton nan a shafin farko na bugunta na ranar Litinin, ta ce Sanata Abdullahi Adamu ya sauka daga mukamin da yake kai.

Abdullahi Adamu ya aika takardar murabus zuwa ga Bola Ahmed Tinubu wanda yanzu haka ya na halartar taron kungiyar AU a kasar Kenya.

Shugaban APC
Shugaban Jam’iyyar APC da Sakatare na kasa Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

Rudani ana daf da taron NEC

Kara karanta wannan

Shugaban APC Na Kasa Adamu Abdullahi Ya Yi Murabus Ne? Ga Abin Da Muka Sani

Wasikar ta isa fadar shugaban kasa a yammacin Lahadi. Sanata Adamu ya bar jama’a a duhu, ya ce ba zai yi magana ba sai shugaban kasa ya dawo.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Murabus din shugaban jam’iyyar ta na zuwa ne a lokacin da ake shirye-shiryen gudanar da taron majalisar koli watau NEC a cikin makon nan.

Sabanin da ake fama da shi ya yi kamari, ta kai Adamu ya fito yana mai shaidawa Duniya cewa bai goyi bayan Tinubu a zaben tsaida gwani ba.

A gefe guda wasu su na zargin tsohon Gwamnan na APC da handamar kudin da aka tara na kamfe, wanda rahotanni sun ce ya kai Naira biliyan 30.

Adamu ya sallama

Kafin a iya gabatar da rahoton binciken kudin da aka yi a majalisar NEC, sai ga jita-jita daga Leadership cewa Adamu zai daina jagorantar NWC.

Kara karanta wannan

Jerin Fitattun Yan Najeriya 4 Da Suka Yi Aiki Da Buhari Kuma Suka Samu Sabbin Mukamai

Ana tunani matsin lamba ne ya yi wa shugaban na APC yawa, hakan ya kai ga ya sauka daga kujerar da ya hau bayan zabe a watan Maris a 2022.

Majiyoyi sun shaidawa Punch cewa shakka babu Adamu ya rubuta wasikar murabus, a gefe guda, wasu sun hakikance a kan akasin hakan.

Wani tsohon hadimi a majalisar wakilai, ya tabbatar da cewa akwai yiwuwar APC tayi sabon shugaba, daga baya ya goge maganarsa a Facebook.

Tolu Ogunlesi wanda ya yi aiki da Muhammadu Buhari, ya yi nuni ga hakan a Twitter, amma daga baya ya ce tambaya ya yi game da rade-radin.

Rigimar APC tayi kamari

A baya an samu rahoto shugabannin Jam’iyya na kasa sun koma musayar kalamai da junansu inda Salihu Lukman ya yi wa Iyiola Omisore raddi.

Lukman ya dade yana sukar yadda jagororinsu su ke rike da APC, a cewarsa Abdullahi Adamu bai aiki da doka, kuma akwai zargin taba kudi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng