Da Dumi-Dumi: Abdullahi Adamu Ya Yi Magana Kan Murabus Dinsa, Ya Bayyana Mataki Na Gaba

Da Dumi-Dumi: Abdullahi Adamu Ya Yi Magana Kan Murabus Dinsa, Ya Bayyana Mataki Na Gaba

  • Rahotanni da dama sun tabbatar da murabus ɗin Sanata Abdullahi Adamu a matsayin shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na ƙasa
  • Wasu daga cikin rahotannin sun tabbatar da cewa Sanata Adamu ya miƙa takardar murabus ɗinsa ne a daren ranar Lahadi, 16 ga watan Yuli
  • Sai dai, Adamu a na shi ɓangaren bai tabbatar da murabus ɗinsa ba, inda ya bayyana cewa ba zai yi magana ba saboda Shugaba Tinubu baya ƙasar

Sanata Abdullahi Adamu ya yi martani kan rahotannin cewa ya yi murabus daga muƙaminsa na shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na ƙasa.

Idan ba a manta ba dai Legit.ng ta kawo rahoto cewa Adamu ya miƙa takardar murabus ɗinsa ne a daren ranar Lahadi, 16 ga watan Yuli wacce aka miƙawa Shugaba Bola Tinubu da shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila.

Kara karanta wannan

Gaskiya Ta Bayyana Kan Dalilin Da Ya Sanya Abdullahi Adamu Ya Rasa Mukamin Shugabancin APC

Abdullahi Adamu ya yi magana kan murabus dinsa
Abdullahi Adamu ya aike da wasikar murabus dinsa zuwa ga Femi Gbajabiamila Hoto: APC Nigeria
Asali: Twitter

Wani majiya wanda ya tabbatar da hakan, ya bayyana cewa:

"Ya yi murabus. Wasiƙar murabus ɗinsa wacce ya rattaɓawa hannu an aike da ita zuwa Villa."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Wasiƙar an aike da ita ne zuwa ga Shugaba Tinubu. Amma tun da shugaban ƙasar yana ƙasar Kenya wajen taron ƙungiyar tarayyar Afirika (AU), an aike da wasiƙar zuwa ga shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa."

Abdullahi Adamu ya yi martani kan rahotannin murabus ɗinsa

A cewar rahoton Daily Trust, an tuntuɓi Adamu domin jin ta bakinsa kan wannan lamarin, inda ya bayyana cewa zai so a ce ya yi magana kan lamarin lokacin da Shugaba Tinubu ya dawo daga wajen taron ƙungiyar AU daga birnin Nairobi na ƙasar Kenya.

"Ba zan yi magana kan lamarin ba saboda shugaban ƙasa baya nan." A cewarsa

Kara karanta wannan

Peter Obi Ya Bayyana Gaskiya Kan Batun Sake Tsayawa Takarar Shugaban Kasa a Shekarar 2027

Dalilin Da Yasa Shugabancin APC Ya Subuce Wa Abdullahi Adamu

A wani labarin kuma, Sanata Abdullahi Adamu wanda rahotanni suka tambayar da ya yi murabus daga shugabancin jam'iyyar All Progressives Congress (APC), ya rasa kujerar ne saboda wasu dalilai.

Tun da farko dai shugaban na APC ya yi takun saƙa da Shugaba Tinubu tun kafin a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa inda ya nuna baya tare da Tinubu a lokacin.

Batun N32bn da ta yi ɓatan dabo a hannun Adamu shi ne dalili na ƙarshe da ya sanya ya yi bankwana da muƙaminsa na shugabancin jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng