Kotu Ta Yi Fatali Da Karar Jam'iyyar AA Kan Zaben Gwamnan Jihar Adamawa
- Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Adamawa ta yi fatali da ƙarar jam'iyyar AA kan nasarar Ahmadu Fintiri
- Kotun ta yi watsi da ƙarar ne bayan jam'iyyar AA da ɗan takararta sun sanar da janyewa daga ƙarar da suka shigar
- Jam'iyyu guda uku ne dai suka shigar da ƙara a gaban kotun domin ƙalubalantar nasarar da Ahmadu Fintiri ya yi a zaɓen gwamnan jihar
Jihar Adamawa - Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Adamawa, ta yi fatali da ƙarar da jam'iyyar Action Alliance (AA) ta shigar inda ta ke ƙalubalantar nasarar gwamna Ahmadu Fintiri.
Jam'iyyar ta AA dai tana ƙalubalantar bayyana gwamnan jihar Ahmadu Fintiri a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamna da aka gudanar a jihar a ranar 16 ga watan Afirilun 2023, cewar rahoton Channels tv.
Jam'iyyar wacce ta shigar da ƙarar ta janye ƙarar a hukumance wanda hakan ya sanya kotun ta yi fatali da ƙarar a zamanta na ranar Juma'a a birnin Yola, babban birnin jihar Adamawa, rahoton Sahel Reporters ya tabbatar.
Jam'iyyu uku na ƙalubalantar nasarar Ahmadu Fintiri a gaban Kotu
Ƙararraki uku aka shigar kan bayyana Fintiri da jam'iyyar PDP a matsayin waɗanda suka yi nasara a zaɓen ta hannun jam'iyyar AA da ɗan takararta, jam'iyyar SDP da ɗan takararta Dr. Umar Ado da jam'iyyar APC da ƴar takararta Sanata Aisha Dahiru Binani.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Binani na neman kotu da ta tabbatar da bayyanata a matsayin wacce ta lashe zaɓen da Hudu Yunusa Ari ya yi.
Kotu ta yi watsi da ƙarar jam'iyyar Action Alliance bayan mai shigar da ƙarar da lauyoyinsu sun sanar da kotun sun janye ƙarar.
Daga Karshe Jam'iyyar APC Ta Yi Magana Kan Gwamnanta Mara Lafiya, Ta Bayyana Lokacin Da Zai Dawo Najeriya
Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da ɗan takararta Fintiri sun shigar da kuɗiri a gaban kotun na ta yi watsi da ƙarar da jam'iyyar APC da ƴar takararta suka shigar.
A ɓangaren jam'iyyar SDP, lauyan jam'iyyar ya kasa kawo hujjoji a gaban kotun. An ɗage sauraron ƙarar har sai zuwa ranar 21 ga watan Yulin 2023.
Binani Ta Sake Kai INEC Kara a Gaban Kotu
A wani labarin kuma, ƴar takarar gwamnan jihar Adamawa a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar APC ta sake kai hukumar INEC ƙara a gaban kotu.
Aisha Dahiru Binani ta kai ƙarar hukumar zaɓen a gaban kotu ne saboda soke sanar da ita a matsayin wacce ta lashe zaɓen gwamnan jihar.
Asali: Legit.ng