Shugaba Tinubu Na Ganawa da Ambode, Gwamna Uba Sani a Aso Villa
- Shugaban kasa, Bola Tinubu ya karɓi bakuncin tsohon gwamnan jihar Legas, Akinwunmi Ambode a Aso Villa ranar Jumu'a
- Haka nan kuma gwamnan Kaduna, Malam Uba Sani ya kai wa shugaba Tinubu ziyara a Villa duk a yau Jumu'a, 14 ga watan Yuli
- Wannan na zuwa ne yayin da ake tsammanin Tinubu ya naɗa ministoci nan da makonni biyu masu zuwa
FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu na gana wa yanzu haka da tsohon gwamnan jihar Legas, Mista Akinwunmi Ambode a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Wannan gana wa ta zo ne bayan shugaban ƙasar ya haɗu da Mista Ambode a wurin liyafar da gwamna Babajide Sanwo-Olu na Legas ya shirya don girmama Tinubu kwanakin baya.
Channels tv ta kawo a rahoto cewa Ambode ya sake dawowa cikin siyasar jihar Legas tsundum tun bayan lokacin da Gwamna Sanwo-Olu ya kai masa ziyara har guda.
Gwamna Sanwo-Olu, mamban jam'iyyar APC ya ziyarci magabancinsa ne domin taya shi murnar cika shekara 60 a duniya ranar 14 ga watan Yuni, 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Menene maƙasudin wannan ziyara da Ambode ya kai wa Tinubu yau Jumu'a?
Bayanai sun nuna cewa shugaba Tinubu na duba yuwuwar naɗa Ambode a wani muƙami na gwamnatinsa yayin da ake dakon ganin mutanen da zai naɗa a matsayin ministoci.
Haka zalika ana hasahen wannan gana wa da shugaba Tinubu ke yi da tsohon gwamnan, zasu karkare tattauna wa kan yuwuwar naɗa Ambode muƙami.
Shugaba Tinubu ya karbi bakuncin gwamnan Kaduna
Bugu da ƙari, shugaban ƙasa Tinubu ya karɓi bakuncin gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani a yau Jumu'a a fadar shugaban ƙasa.
A 'yan kwanakin nan gwamnan Kaduna ya gana da manyan hafsoshin tsaron ƙasa 3 da mai ba da shawara kan tsaro na ƙasa, Nuhu Ribadu.
Uba Sani ya yi wannan zama a lokuta daban-daban da mutanen ne a yunkurinsa na ganin zaman lafiya mai ɗorewa ya dawo a jihar Kaduna.
Gwamna Nwifuru Ya Kara Wa Ma'aikata Albashi a Jihar Ebonyi
Wani rahoton ya nuna cewa Gwamna Francis Nwifuru na jam'iyyar APC ya ƙara wa ma'aikatan jihar Ebonyi albashin domin rage masu raɗaɗin cire tallafin mai.
Nwifuru, ya amince da ƙarin albashin naira N10,000 ga kowane ma'aikacin jiha ba tare da la'akari da matakin aiki ba.
Asali: Legit.ng