El-Rufai Da Wasu Da Suka Ki Amsar Tayin Zama Ministocin Shugaban Kasa Tinubu

El-Rufai Da Wasu Da Suka Ki Amsar Tayin Zama Ministocin Shugaban Kasa Tinubu

  • Yan Najeriya na ci gaba da zaman jiran ganin wadanda Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai nada mukaman ministoci makonni shida bayan hawa kujerar mulki
  • Wasu fitattun yan siyasa sun ce ba za su karbi mukaman ministoci ba koda Shugaban kasa Tinubu ya yi masu tayi
  • Jigon PDP, Bode George da Ayodele Fayose da kuma tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai sune yan kadan daga cikin jerin mutanen

Yayin da yan siyasa da dama ke ta kamun kafa domin samun shiga cikin jerin ministocin Shugaban kasa Bola Tinubu, wasu sun fito karara sun nuna basa sha'awar wannan matsayi karkashin gwamnati mai ci.

Har yanzu shugaban kasa Tinubu bai aikawa majalisar dokokin tarayya jerin ministocinsa ba tun bayan da ya hau karagar mulki a ranar Litinin, 29 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

Bayanai Sun Fito: An Bayyana Wanda Shugaba Tinubu Ya Ke Son Nada Wa Minista Daga Jihar Ogun

Fayose, George, El-Rufai sun ki karbar tayin zama ministocin Tinubu
El-Rufai Da Wasu Da Suka Ki Amsar Tayin Zama Ministocin Shugaban Kasa Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu/ Nasir El-Rufai/TZAR Foundation
Asali: Facebook

Jigon PDP Cif Olabode George ya ce ba zai iya zabar mutane

Daya daga cikin mutanen da suka ki tayin aiki a matsayin minista karkashin gwamnatin Tinubu shine tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP)na kasa Cif Olabode George.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kamar yadda jaridar Punch ta rahoto, George ya ce shi ya yi tsufa da neman mukamin minista a wannan mataki na rayuwarsa.

Sai dai kuma, George ya bayyana cewa zai dai iya taimakawa wajen zabo yan takara da suka cancanta idan aka tunkare shi ko aka gabatar masa da nmukamin.

"Zan ba shi mutanen da suke da ilimin daga jam'iyyar kasancewana manajan jam'iyyar na tsawon shekaru. Idan ya ce yana so na taimaka masa wajen samo wani, akwai miliyoyin matasa da suke da karfin kaiwa da komowa ba irina ba.

"Ba nawa bane, saboda ba neman aiki nake yi ba. Amma idan ya kira ni, za mu tattauna batun a gaban shugabannin jam'iyyar, mu hada kai sannan mu zabo daga bangarenmu mutum da yake da jini a jika, mai karfi, wanda ke da ilimi kuma wanda zai iya kawo ci gaba ga kasar nan."

Kara karanta wannan

Yanzu nan: Shugaban APC Ya Hakura da Rikon Jam’iyya, Ya Sauka Daga Kujerarsa

Tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya ce ba zai karbi mukamin ministan Abuja ba

Wani shahararren dan siyasa shine tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, wanda ya ce ba zai sake amsar tayin ministan babban birnin tarayya ba.

El-Rufai ne ministan babban birnin tarayya a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo.

Sai dai kuma, bai yi magana kan ko zai amsa ko ba zai amsa tayin zama minista ba idan shugaban kasar ya ba shi wani aiki na daban, Daily Trust ta rahoto.

"Koda an yi mun tai, ba zan zo Abuja ba. Kamar yadda na fadi, a zan taba maimaita aji ba kuma akwai matasa da dama da na sani da zan iya gabatar da su wadanda za su yi aiki fiye da yadda nayi a matsayin ministan Abuja.
"Na yi tsufa sosai da wannan. Na yi tsufa da rusau, ku nemo matashi mai jini a jika ko matashiya."

Kara karanta wannan

Nesa Ya Zo Kusa: Shugaban Kasa Tinubu Zai Bayyana Jerin Sunayen Ministocinsa a Wannan Makon, An Yi Karin Bayani

Tsohon gwamnan Ekiti Ayodele Fayose ya ce ba zai karbi mukamin minista ba

Tsohon gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose ya ce ba zai karbi tayin mukamin ministan Tinubu ba idan har aka ba shi.

Fayose ya bayyana hakan ne a yayin wata hira da Channels TV, a shirin Sunday Politics, a Abuja a ranar Lahadi, 9 ga watan Yuli.

Jigon na PDP ya ce "Ba zan taba karba ba."

APC ta magantu kan yiwuwar ba Kwankwaso da Wike mukamin minista a gwamnatin Tinubu

A gefe guda, Legit.ng ta kawo a baya cewa Sanata Iyiola Omisore, babban sakatern jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, bai yi watsi da yiwuwar sanya sunayen manyan yan jam'iyyun adawa kamar su Nyesom Wike da Rabiu Musa Kwankwaso a matsayin ministocin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ba.

Da yake zantawa da Channels TV a shirin Politics Today a ranar Talata, 11 ga watan Yuli, Omisore ya ce jam'iyya mai mulki na iya "fitowa da majalisa ta hadin shinkafa da wake".

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng