Kotun Zabe Za Ta Yanke Hukunci Kan Karar da Aka Nemi Tsige Shugaba Tinubu

Kotun Zabe Za Ta Yanke Hukunci Kan Karar da Aka Nemi Tsige Shugaba Tinubu

  • Mai shari'a Haruna Tsammani na Kotun suraron ƙarar zaben shugaban ƙasa ya jingine hukunci kan karar jam'iyyar APM
  • APM ta buƙaci Kotu ta soke zaben da Tinubu da Shettima suka samu nasarar zama shugaban ƙasa da mataimaki
  • A ƙorafin jam'iyyar, ta ce ya kamata a soke tikitin Tinubu da Shettima saboda mataimakin shugaban ya nemi kujera biyu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaben shugaban ƙasa ta jingine hukuncin da zata yanke zuwa ranar zama na gaba da zata sanar nan gaba kan ƙarar da jam'iyyar APM ta shigar.

A ƙarar da ta shigar, jam'iyyar Allied Peoples Movement (APM) ta roƙi Kotun ta rushe zaben da ya bai wa shugaban ƙasa, Bola Tinubu, da Kashim Shettina nasara a watan Fabrairu.

Kashim Shettima tare da shugaba Tinubu a wurin kamfenn APC.
Kotun Zabe Zata Yanke Hukunci Kan Karar da Aka Nemi Tsige Shugaba Tinubu Hoto: Bola Ahmed Tinubu, Kashim Shettima
Asali: Facebook

APM ta nemi soke zaɓen ne bisa hujjar da ta dogara da ita cewa mataimakin shugaban ƙasa, Shettima, bai cancanci shiga takara ba a zaɓen, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Biliyan N2.9: Babbar Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Tsohon Gwamnan Da Ake Zargi Da Karkatar da Kuɗaɗen Jiha

Meyasa APM take son Kotu ta tsige Tinubu da Shettima?

A cewar ƙorafin jam'iyyar APM, ya haramta Shettima ya shiga zaɓe saboda ya nemi tikitin takara biyu, mataimakin shugaban ƙasa da Sanata kuma duk a babban zaɓe ɗaya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mai shari'a Haruna Tsammani, wanda ke jagorantar kwamitin alkalan Kotun ya ce sun jingine hukunci kan ƙorafin APM zuwa lokacin da za a sanar da jam'iyyun nan gaba.

Ya ce Kotu tana son bayyana hukuncin da ta yanke kan ƙarar APM a ranar da zaɓi yanke hukuncin kan ƙararrakin Atiku Abubakar/PDP da kuma ta Peter Obi/LP.

Kotun ta ɗauki wannan matsaya ne bayan jam'iyyun sun aminta da rubutaccen bayaninsu na ƙarshe da safiyar ranar Jumu'a, 14 ga watan Yuli, 2023, inji rahoton Punch.

Jerin waɗanda APC ta shigar ƙara

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Gana da Jiga-Jigai a Villa, Ya Faɗi Yadda Ya Zama Shugaban ECOWAS

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), Jam'iyyar APC, Tinubu, Shettima da Kabir Masari (wanda ya riƙe wuri kafin zaɓo Shettima) su ne waɗan APM ke ƙara na ɗaya, na biyu, na uku, na huɗu da na biyar bi da bi.

Ana zargin Shettima ya karɓi Fom ɗin neman takarar Sanatan Borno ta tsakiya kafin shugaba Tinubu ya zaɓe shi a matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa.

Babbar Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Tsohon Gwamnan Da Ake Zargi da Almundahana

A wani labarin kun ji cewa Babbar Kotun Abuja ta kori ƙarar da aka shigar da tsohon gwamnan jihar Imo, Sanata Rochas Okorocha.

Alkalin Kotun ya ce tuhumar da EFCC ke yi wa Sanata Okorocha raina shari'a ne saboda hukumar ta shigar da makamanciyar wannan kara kan wanda ake zargi a babbar Kotun tarayya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262