Tinubu Ya Gano Hanyar Wargaza LP, Zai Ba Na-Hannun Daman Peter Obi Kujerar Minista
- Daniel Bwala ya firgita magoya bayan Peter Obi bayan ya ce ana shirin raba kan jam’iyyar LP
- Lauyan wanda jagora ne a PDP ya ce za a ba wani ‘dan kwamitin LP-PCC mukamin Minista
- A cewar Bwala, wanda aka yi wa wannan tayi ya yi watsi da alakarsa da Obi, zai karbi kujerar
Abuja - Jigo a jam’iyyar PDP, Daniel Bwala ya fito ya na cewa Bola Ahmed Tinubu yana yunkurin raba kan jam’iyyar adawar nan ta LP.
Da yake magana a shafin Twitter a ranar Alhamis, Daniel Bwala ya ce Shugaban kasan ya shirya ba wani babba a LP mukami mai tsoka.
Mai magana da yawun Atiku Abubakar a zaben 2023 yake cewa burin Bola Tinubu shi ne ya kawo rabuwar kai tsakanin ‘yan adawan na sa.
A cewarsa, tuni har wannan ‘dan siyasa ya amine da tayin Mai girma shugaban kasa, ya amince ya karbi kujerar Minista a gwamnatin tarayya.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Gajeren jawabin Bwala bai kama sunan jigon jam’iyyar LP da zai shiga gwamnatin Tinubu ba. Jaridar Daily Post ta kawo labarin nan a jiya.
Legit.ng Hausa ta fahimci maganar da tsohon jagoran na jam’iyyar APC mai-mulki ya yi, ya bar mutane su na ta faman waiwaye a cikin duhu.
Maganar Daniel Bwala
“An rahoto cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana so ya jawo cikas a bangaren jam’iyyar LP
Zai nada wani daga cikin manyan ‘yan kwamitin yakin neman zaben Peter Obi a matsayin Minista. Ana cewa wannan mutumi ya amince.”
- Daniel Bwala
An bar magoya baya a duhu
Wani mai suna Keji Akinwale a dandalin na Twitter, yana da ra’ayin cewa ba kowa ba ne wannan illa Farfesa Utomi, jigo a jam’iyyar LP.
Wani masoyin ‘dan takaran na LP a zaben shugaban kasan bana ya ce ko mai zai faru, ba za su juyawa gwaninsu. Peter Gregory Obi baya ba.
Irinsu wani da ya kira kan shi Mista Incredible ya ce watakila Lamidi Apapa ne za a ba Ministan kwadago, ya maye gurbin Festus Keyamo.
A gefe guda, wasu masoyan LP sun ce saura kiris kotun karar zabe ta ba Peter Obi nasara.
Addini wajen zaben shugabanni
Da yake jawabi a Legas, an rahoto tsohon Gwamna Kaduna, Nasir El-Rufai ya ce Kiristoci sun fi samun mukamai a gwamnatin Bola Tinubu.
El-Rufai ya na da ra'ayin cewa masu kaushin addini da wadanda ke hasashen nasarar Peter Obi sun kunyata a 2023 da APC ta samu nasara.
Asali: Legit.ng