Fitaccen Mai Sukar Yan Siyasa Ya Yi Hasashen Sakamakon Shari'ar Kotun Zaben Shugaban Kasa
- An shaidawa Peter Obi da Atiku Abubakar cewa ba za su sami nasara kan Shugaba Bola Tinubu ba a kotun sauraron kararrakin zabe
- Wannan shi ne hasashen da Deji Adeyanju, wani mai fafutukar kare hakkin bil'adama kuma mai sharhi kan harkokin siyasa ya yi
- Ya yi hasashen cewa kotun za ta yi watsi da karar Atiku da Obi a wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Tuwita ranar Laraba, 12 ga watan Yuli
Dan rajin kare hakkin bil’adama kuma lauya Deji Adeyanju, ya ce kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa da ke ci gaba da gudanar da shari’a kan zaben shugaban kasa, za ta yanke hukuncin da zai yi wa Bola Tinubu dadi.
Idan ba a manta ba, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da Peter Obi na jam’iyyar Labour, suna kalubalantar nasarar da Tinubu ya samu a zaben shugaban kasa na ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairun 2023.
Kotu za ta yi fatali da karar Atiku da Peter Obi
Adeyanju ya bayyana hasashen nasa ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Tuwita a ranar Laraba, 12 ga watan Yuli.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cikin sakon, Adeyanju ya bayyana cewa kotun sauraron kararrakin zabe za ta yi watsi ne da karar da Atiku Abubakar da Peter Obi suka shigar.
Adeyanju ya shahara sosai wajen bayyana ra’ayoyinsa na siyasa musamman ma dai a kafafen sada zumunta.
Masu amfani da kafar sada zumunta sun yi wa Adeyanju martani mai zafi
Hasashen nasa dai ya gamu da ra'ayoyi mabanbanta, inda wasu masu sharhi kan batutuwan siyasa suka aminta da hasashen nasa, wasu kuma sun ki yarda da hasashen na Adeyanju.
@rilwan_ola01 ya ce:
"Da alama INEC ta sanyaka cikin tsari, kamar yadda muka ji a makonnin da suka gabata cewa za ta ci gaba da daukar nauyin wasu mutane masu tarin mabiya domin su ci gaba da wallafa rubutu irin wannan."
Yanzu: Zullumi Yayin Da Ake Jiran Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Makomar Ministan Buhari, Abubakar Malami
@kasalimi2029 ya ce:
"Sakarai, idan da za a yi watsi da ita ba za ta kai ga wannan matakin ba, ni ba dan PDP ba ne, amma a matsayinka na wanda yake cikin PDP, ya kamata a ce kana da kwarin gwiwa."
Shehu Sani ya yi hasashen abinda zai faru idan kotu ta tsige Shugaba Tinubu
Legit.ng a baya ta kawo wani rahoto kan hasashen da tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Kwamared Shehu Sani ya yi dangane da shari’ar zaben shugaban kasa da ke gudana a yanzu.
Ya ce idan kotun sauraron kararrakin zabe ta tsige Tinubu, to ya shiryawa maganganu marasa dadi daga wani tsohon gwamnan jihar Kaduna.
Asali: Legit.ng