‘Yan Siyasa Sun Raba Hankalin Tinubu, Za a Rasa Wanda Zai Zama Minista Daga Bauchi

‘Yan Siyasa Sun Raba Hankalin Tinubu, Za a Rasa Wanda Zai Zama Minista Daga Bauchi

  • Idan dai so samu ne, Disciples of Jagaban (DoJ) za ta yi sha’awar ganin Isa Yuguda ya zama Minista
  • Shugaban kungiyar na reshen Bauchi, Hussani Suleman yana so a tuna da tsohon Gwamnan na su
  • Bola Tinubu zai sha wahala wajen dauko wanda zai wakilci jihar Arewa maso gabashin din a FEC

Bauchi – Shugaban wata kungiya ta Disciples of Jagaban (DoJ) ta reshen jihar Bauchi, Hussani Suleman ya shiga maganar nadin sababbin Ministoci.

A rahoton This Day na ranar Laraba, an ji shugaban kungiyar DoJ ta Mabiya Bola Ahmed Tinubu yana, Alhaji Hussani Suleman yana tallata Isa Yuguda.

Jagoran kungiyar magoya bayan ya ce a cikin wadanda ake maganar za a dauko a matsayin Minista daga Bauchi, Malam Isa Yuguda duk ya fi su cancanta.

Bola Tinubu a Aso Rock
Bola Tinubu bai nada Ministoci ba Hoto: @ABATMediaCentre
Asali: Twitter

Ya aka yi Yuguda ya yi zarra?

Kara karanta wannan

Wasu Darusa 4 Da Aka Fahimta Daga Nasarar Tinubu Da Shettima a Zaben 2023, El-Rufai

Suleman yake cewa tsohon Gwamnan yana da farin-jini da shahara a siyasa, bayam haka ya taka rawar gani domin Bola Tinubu ya yi nasara a zaben 2023.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Baya ga kokarin da ya yi wa APC a Arewacin Najeriya a zaben bana, DoJ ta ce Yuguda ya taba rike kujerar Ministan sufuri da harkokin jiragen sama a baya.

A lokacin da ya yi Gwamna na shekara takwas, kungiyar ta ce mutanen jihar Bauchi sun yaba. Sai dai Legit.ng Hausa ta fahimci kujerar nan sai mai rabo.

Pate zai sake zama Minista?

Watakila Yuguda zai gwabza da Dr. Musa Babayo, Yusuf Maitama Tugga, Bala Jibrin da irinsu Farfesa Mohammed Pate wajen samun wannan mukami.

Mohammed Pate ya samu kujera da ake ji da ita a Duniya, amma ya hakura. Wasu su na ganin hakan bai rasa nasaba da harin sake zama Ministan lafiya.

Kara karanta wannan

Yanzu: Shugaba Bola Tinubu Na Shirin Nada Tsohon Hadiminsa Mukami Mai Muhimmanci

Babayo tsohon jigo ne a PDP yayin da Tugga ya taba zama Jakada zuwa Jamus. Kuma ba za a rasa wasu 'yan APC da ke harin kujerar nan a Bauchi ba.

Ganin jam’iyyar APC ta sake rasa zaben Gwamna a bana, magoya bayan Air Marshal Abubakar Siddique mai ritaya za su so a saka masa da kujera a FEC.

Tsohon shugaban hafsun sojojin saman ne ya yi wa jam’iyyar APC takara, amma bai iya karbe mulki daga hannun Gwamna mai-ci, Bala Mohammed ba.

Wa ya dace ya zama Minista?

Mun tambayi wani matashin ‘dan siyasa a jihar Bauchi ko wa ya fi dacewa da matsayin nan, sai ya ce wadanda suka dace mutane uku ne;

1. Amb. Yusuf Tuggar: Saboda shi kadai ne ‘dan siyasar da yaci karamar hukumar shi a APC a duk zaben da aka yi. Kuma ya ci ‘Dan Majalisar tarayya da na jiha a shiyyar shi.

Kara karanta wannan

An Ji Yadda Gwamnan PDP Ya Taimaki APC, Bola Tinubu Ya Zama Shugaban Kasa

Shine ‘dan APC da bai taba fita ko yin zagon kasa a jam'iya domin bai samu abinda yake nema ba.

2. Dr Musa Babayo: Shi yayi aiki a matsayin mai tsare-tsare a kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa. Talban Katagum yayi hidima ga APC kuma yayi takaran Gwamna, ko da ya fadi a zaben fitar da gwani, ya tsaya a APC.

3. Dr. Nura Manu Soro: Sai lokacin da ya karbi jagorancin tafiyar Tinubu ne, aka fara yi wa APC yakin neman zaben Shugaban kasa a jihar Bauchi. Kafin nan kawai yaudara ake yi, duk bai samu tikiti ba, yayi kokari wajen taimakon ‘yan APC a zabe.

Wannnan ‘dan siyasa da ya nemi a sakaya sunansa ya ce mutanen da ake magana sun cancanta, sai su na neman wanda zai iya farfado da APC.

A cewarsa akwai bukatar wanda zai zama Minista, ya tafi da kowane bangare a matsayin na shi.

Darasi daga zaben 2023

Kara karanta wannan

Rade-Radin Minista: Jigon NNPP a Kano Ya Karyata Labarin Samun Mukami a Tarayya

Rahoto ya zo cewa Nasir El-Rufai ya ce Kiristoci sun fi samun mukamai a gwamnatin Bola Tinubu da aka zarga da fitita Musulunci a lokacin yakin zabe.

Daga yanzu, tsohon Gwamnan Kaduna ya ce kyau a daina waiwayen addini a zabe, ya kuma ce masu hasashen nasarar Peter Obi sun kunyata a 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng