Jerin Ministocin Tinubu: “A Karshe, Yan Najeriya Za Su Ji Dadi”, Omisore Ya Ba Da Tabbaci

Jerin Ministocin Tinubu: “A Karshe, Yan Najeriya Za Su Ji Dadi”, Omisore Ya Ba Da Tabbaci

  • Babban sakataren jam'iyyar APC, Sanata Iyiola Omisore ya yi martani kan rade-radin nada manyan yan jam'iyyun adawa a majalisar shugaban kasa Bola Tinubu
  • Omisore ya yi martani ne da aka yi masa tambaya kan ko Shugaban kasa Tinubu zai nada tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, a matsayin minista
  • Wike ya yi wa Tinubu aiki a zaben shugaban kasa na 2023 lokacin yana a matsayin gwamna karkashin inuwar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP)

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Senata Iyiola Omisore, babban sakatern jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, bai yi watsi da yiwuwar sanya sunayen manyan yan jam'iyyun adawa kamar su Nyesom Wike da Rabiu Musa Kwankwaso a matsayin ministocin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ba.

Da yake zantawa da Channels TV a shirin Politics Today a ranar Talata, 11 ga watan Yuli, Omisore ya ce jam'iyya mai mulki na iya "fitowa da majalisa ta hadin shinkafa da wake".

Kara karanta wannan

Yanzu: Shugaba Bola Tinubu Na Shirin Nada Tsohon Hadiminsa Mukami Mai Muhimmanci

Akwai yiwuwar baiwa yan adawa mukami a majalisar Tinubu
APC Ta Magantu Kan Sanya Sunayen Wike Da Kwankwaso a Jerin Ministocin Shugaban Kasa Bola Tinubu Hoto: @OfficialAPCNg, @GovWike, @KwankwasoRM
Asali: Twitter

Jerin ministocin Bola Tinubu: "Muna iya fitowa da hadaddiyar majalisar ministoci", inji APC

Sai dai kuma, ya bayyana cewa ana kan tattaunawa tsakanin shugaban kasar da kwamitin aiki na jam'iyya mai mulki na kasa dangane da jerin sunayen ministocin na karshe, Daily Trust ta rahoto.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Da aka tambaye shi ko shugaban kasa Tinubu zai kafa gwamnati ta hadin kan kasa da mambobin jam'iyyun adawa kamar su Wike, tsohon gwamnan jihar Ribas (dan jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP), da Kwankwasi (jigon jam'iyyar NNPP), Omisore ya ce wuka da nama na a hannun shugaban Najeriyan.

Kalamansa:

“Akwai masu fasaha wadanda suke yan siyasa ne. Wasu daga cikin mu, mu kwararru ne. Mun karantu a bangaren ilimi. Don haka mu yan siyasa masu ilimin fasaha ne.
"Da zaran mun duba lamarin tare da kuma abun da zai amfani yan Najeriya sosaim za mu iya fito da majalisar ministoci ta shinkafa da wake wanda za ku ji dadinsa."

Kara karanta wannan

An Ji Yadda Gwamnan PDP Ya Taimaki APC, Bola Tinubu Ya Zama Shugaban Kasa

Fayose ya yi gaskiya da ya kira Wike da karamin mahaukaci, Hadimin Atiku

A wani labarin, Phrank Shaibu, kakakin tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, ya ce tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya yi daidai da ya bayyana tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike a matsayin "karamin mahaukaci".

Shuaibu ya bayyana haka ne a wata sanarwa da aka gabatarwa Legit.ng a ranar Litinin, 10 ga watan Yuli da yake martani ga hirar da aka yi da Fayose a gidan talbijin na Channels a shirin dare, 'Sunday Politics'.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng