APC a Shirye Take Ta Karbi Mambobin Tawagar G-5 Zuwa Inuwarta, Adamu
- Abdullahi Adamu ya bayyana matsayar jam'iyyar APC dangane da raɗe-raɗin sauya sheƙar tawagar gwamnonin G-5
- Shugaban APC na ƙasa ya ce a shirye su ke kuma zasu tarbi G-5 karkashin Nyesom Wike hannu biyu idan suka zaɓi sauya sheka
- Ya kuma musanta raɗe-raɗin cewa alaka ta yi tsami tsakaninsa da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT Abuja - Shugaban APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya ce jam'iyya mai mulki a shirye take ta karɓi tawagar gwamnonin G-5 karkashin jagorancin Nyesom Wike.
Sanata Adamu ya bayyana haka ne yayin hira da Arise TV ranar Talata, 11 ga watan Yuli, 2023.
Shugaban APC ya ce jam'iyyar zata yi farin ciki da maraba da tawagar G-5 a duk lokacin da suka yanke sauya sheƙa daga PDP zuwa APC mai mulƙin Najeriya.
Shugaba Tinubu Ya Dau Zafi Kan Kashe-Kashen Da Ake Yi a Jihohin Plateau Da Benue, Ya Ba Jami'an Tsaro Muhimmin Umarni 1
Gabanin zaɓen 2023, gwamnonin PDP 5 na jihohin Ribas, Enugu, Oyo, Benuwai da Abiya sun kafa tawagar G-5 kana suka yaƙi ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP, Atiku Abubakar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Huɗu daga cikinsu sun sauka daga kujerunsu bayan kammala wa'adi biyu ranar 29 ga watan Mayu, yayin da Seyi Makinde na jihar Oyo ya samu nasarar tazarce.
Shin dagaske Shugaba Tinubu da Adamu basu ga maciji?
Haka nan kuma Adamu ya musanta jita-jitar da ake yaɗawa cewa alaƙa ta yi tsami tsakaninsa da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Jaridar Vanguard ta rahoto Adamu na cewa wannan raɗe-raɗin ba shi da tushe ballantana makama, duk kanzon kurege ne.
Sai dai ya bayyana cewa gabanin Tinubu ya lashe tikitin takarar shugaban ƙasa, yana da 'yancin goyon bayan kowane ɗan takara wanda ya kwanta masa a rai.
Shugaban APC ya kara da cewa kamata ya yi a yaba masa bisa jagorantar jam'iyar ta gudanar da zaben fidda gwani cikin nasara da kuma nasarar Bola Tinubu.
A kalamansa, Sanata Adamu ya ce:
"Ina tunanin kun ɗauki batun ne domin kasuwarku yan jarida. Dagaske ne na bayyana sunan Sanata Ahmad Lawan a matsayin ɗan takarar maslaha ga kwamitin gudanarwa (NWC)."
"Wannan ya faru kafin babban taro, abubuwa da dama sun biyo baya daga lokacin da na faɗi haka zuwa ranar babban taron zaɓen fidda gwani kuma kun ga yadda ta kaya a wurin bisa jagoranci na."
"Washe gari na jagorancin mambobin NWC muka je wurin Tinubu a gidansa na Asokoro muka tabbatar masa da goyon baya kuma muka ce zamu yi aiki kafaɗa da kafaɗa don tabbatar da 'yan Najeriya sun karɓe shi."
Bugu da ƙari, shugaban APC ya ce bayan haka jam'iyyar ta lashe babban zaben shugaban ƙasa amma maimakon a yaba masa, sai aka koma shirya musu tuggu.
Shugaba Tinubu Zai Nada Ministoci 36 Zuwa 42 a Gwamnatinsa, Omisore
A wani labarin na daban kuma Sakataren APC na ƙasa ya bayyana yawan ministocin da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, zai naɗa a sabuwar gwamnati.
Kundin tsarin mulkin Najeriya ya tilasta wa shugaban ƙasa ya naɗa minista ɗaya daga kowace jiha a Najeriya da kuma ƙarin minista ɗaya daga kowace shiyya.
Asali: Legit.ng