Yadda Sabon Tsarin Tinubu Ya Tilasta Gwamnonin PDP Biyu Rage Yawan Ma'aikatu
- Tsige tallafin man fetur da Shugaba Bola Tinubu ya yi ya tilasta wasu gwamnoni tsuke bakin aljihun jihohinsu
- Aƙalla gwamnoni biyu na PDP sun ji a jika a dalilin cire tallafin inda suka sanar da rage yawan ma'aikatun jihohinsu
- Sabbin gwamnonin na jam'iyyar PDP su ne Dauda Lawal Dare na jihar Zamfara da Agbu Kefas na jihar Taraba
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Sanar da cire tallafin man fetur da shugaba Tinubu ya yi a ranar Litinin 29 ga watan Mayu, ya tilasta hukumomi da mutane da dama sauya tsarinsu domin rage raɗaɗin da cire tallafin ya haifar.
Ƙalubalen har jihohi bai ɗaga wa ƙafa ba, musamman wasu daga ciki na jam'iyyar PDP inda suka sanar da sauye-sauye domin tabbatar da ayyukansu na tafiya yadda ya dace a cikin matsin tattalin arziƙin da ake ciki.
Dalilin da ya sanya wasu gwamnonin PDP suka rage yawan ma'aikatunsu
Wasu daga cikin gwamnonin PDP sun nuna sun ji a jika a dalilin cire tallafin man fetur, wanda hakan ya sanya su suka rage yawan abinda su ke kashewa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Domin rage yawan fitar da kuɗi, jihohin da lamarin ya shafa sun sanar da rage yawan ma'aikatu a jihohinsu.
Abun lura shi ne, gwamnonin da suka ɗauki wannan hukuncin ƙasa da wata biyu bayan Shugaba Tinubu ya cire tallafin, wannan ne karonsu na farko a matsayin gwamnoni.
Dauda Lawal
Sabon gwamnan na jihar Zamfara ya rage yawan ma'aikatun jihar daga 28 zuwa 16 a ranar 7 ga watan Yuli.
Gwamnan ya sanar da hakan ne a cikin wata sanarwa da babban darektan watsa labarai na ofishin gwamnan, Nuhu Anka, ya fitar.
Cire Tallafin Man Fetur: Manyan Matsaloli 4 Da 'Yan Najeriya Ke Kuka Da Su Bayan Tinubu Ya Tsige Tallafi
Agbu Kefas
Kefas shi ma wani sabon gwamnan PDP ne da ya sanar da rage yawan ma'aikatun jiharsa daga 25 zuwa 21.
Gwamnan ya sanar da hakan ne a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis, 6 ga watan Yuli.
Gwamnan Taraba Ya Rage Kudin Karatu a Jami'ar Jihar
A wani labarin kuma, gwamnan jihar Taraba ya sanar da rage kuɗin karatun da ɗalibai ke biya a jami'ar jihar.
Gwamna Agbu Kefas ya sanar da zaftare kuɗin da kaso 50% a dalilin cire tallafin man fetur da gwamnatin Shugaba Tinubu ta yi.
Asali: Legit.ng