An Ji Yadda Gwamnan PDP Ya Taimaki APC, Bola Tinubu Ya Zama Shugaban Kasa
- Tony Okocha bai hakura da alfarmar da yake nema a wajen Bola Tinubu idan an tashi raba Ministoci ba
- Jagoran na APC ya ce goyon bayan Nyesom Wike ne kawai ya yi sanadiyyar nasararsu a Ribas a 2023
- Idan da tsohon Gwamnan ya goyi bayan jam’iyyarsa a zaben shugaban kasa, to Peter Obi ne zai yi galaba
Abuja - Tsohon shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin Ribas, Tony Okocha ya ce gudumuwar Nyesom Wike ta taimaka masu a zaben 2023.
The Nation ta rahoto Cif Tony Okocha yana bayanin yadda tsohon Gwamnan na Jihar Ribas ya taimakawa yakin neman zaben Bola Ahmed Tinubu.
Saboda kokarin da ya yi masu a zabe ne Okocha yake neman alfarma wajen shugaban kasa, ya ware kujerar Minista, ya ba Nyesom Wike.
A cewar ‘dan siyasar kuma jigo a APC, Wike ya bada gudumuwa na gaske da kuma tallafin kudi saboda ganin Bola Tinubu ya lashe zaben bana.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Da yake zantawa da manema labarai a garin Abuja, Okocha ya ce ba don tsohon Gwamnan ba, da Peter Obi da jam’iyyar LP ne za su yi nasara.
"Abin da na ke cewa shi ne a cikin tsohon mai gidana, Rotimi Amaechi da mutanensa da Sanata Magnus Abe, babu wanda ya yi wa Tinubu aiki.
Abin da yake taimake mu a jihar Ribas shi ne sakarcin PDP. Kamar yadda mu ka sani, a lokacin Nyesom Wike ne yake rike da akalar jihar ta wa.
Tun da aka kafa PDP a 1998, jam’iyyar ta ke samun nasara a jihar Ribas. Ta lashe duk wasu zabuka da aka yi, har a lokacin da mu ke rike da gwamnati.
- Tony Okocha
Sun ta ce jagoran na APC ya shaida cewa Wike ya bada umarnin cewa ‘ya ‘yan PDP su yi aiki da jam’iyya mai mulki a sama a zaben shugaban kasa.
Babu Amaechi, babu Abe a APC
Tun da su ne a jam’iyyar APC a lokacin, Okocha ya ce shi ya yi aiki da magoya bayan Wike a 2023 a lokacin da Amaechi da Abe su ka yi watsi da su.
"Abe ya tafi SDP, Amaechi bai yi niyya ba. Zan iya bugun kirji in fada da cewa Wike ya dauki dawainiyar 70% na zaben nan, shi ya yi mana komai.
Ba don gudumuwar kaya da kudin Wike ba, da Peter Obi zai yi nasara a jihar Ribas."
-Tony Okocha
Su wa za a ba Ministoci?
Idan an tashi rabon Ministoci, an ji labari jam’iyyar APC ta ce za a dauko mutane na dabam, wadanda su ka san aiki kuma za su maida hankali sosai.
Iyiola Omisore ya ce ba a fito da sunayen Ministocin ba tukun, su na cigaba da tattaunawa, ana yanke shawara da Bola Tinubu ne game da batun.
Asali: Legit.ng