Fayose Ya Yi Daidai Da Ya Bayyana Wike a Matsayin ‘Karamin Mahaukaci’ – Hadimin Atiku
- Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose ya bayyana tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike a matsayin "karamin mahaukaci"
- Hadimin Atiku Abubakar, Mista Phrank Shaibu, ya jadadda hakan a cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Litinin, 10 ga watan Yuli
- Shaibu ya kuma caccaki gwamninin G-5, inda ya bayyana su a matsayin yan siyasa marasa amfani da ke neman suna
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja - Phrank Shaibu, kakakin tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, ya ce tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya yi daidai da ya bayyana tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike a matsayin "karamin mahaukaci".
Shuaibu ya bayyana haka ne a wata sanarwa da aka gabatarwa Legit.ng a ranar Litinin, 10 ga watan Yuli da yake martani ga hirar da aka yi da Fayose a gidan talbijin na Channels a shirin dare, 'Sunday Politics'.
A wata hira da aka yi da shi, an tambayi Fayose ko Wike zai dace da majalisar Shugaban kasa Bola Tinubu duk da kasancewarsa dan adawa, sai ya ce:
"Wike mutum ne mai iya magana. Najeriya na bukatar mutum mai karamin hauka."
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A farkon Mayun 2022, Wike, yayin ziyarar da ya kai jihar Kogi, ya bayyana cewa Najeriya na bukatar mahaukaci domin kula da harkokinta.
“Zan iya dawo da kasar nan kan tafarkinta na daukaka. Ba dole sai an damu daga inda ka fito ba. Mahaukaci ne zai iya mulkin Najeriya.”
Da yake martani ga hirar Fayose, Shaibu ya ce nada Wike a matsayin minista daidai yake da barin mahaukaci ya samu mafaka.
Ya ce:
"Muna son yaba ma Fayose da ya bayyana Wike a matsayin wani "karamin mahaukaci". Shakka babu, mahaukaci ne kawai zai iya amfani da tashin hankali wajen hana mutane zuwa kamfen a wata jiha. Hauka ce kawa za ta iya hana muradin mutane."
Hadimin Atiku ya yi wa gwamnonin G-5 wankin babban bargo
Shaibu bai kyale tsoffin gwamnonin G-5 ba, wadanda ya bayyana a matsayin yan siyasa marasa amfani da suka zama masu kamun kafa.
Ya ce tsoffin gwamnonin na neman mafaka daga hukunci da mukamai don a ci gaba da damawa da su.
Shaibu ya bayyana tsohon gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom a matsayin gwamna da ya fi kowa lalacewa a tarihin Najeriya.
PDP ta kira taron gaggawa, gwamnonin jam'iyyar za su yi kus-kus
A gefe guda, Legit.ng ta rahoto a baya cewa kungiyar gwamnonin PDP ta kira wani taron gaggawa a Abuja.
Za su tattauna batutuwan da ke faruwa a kasar karkashin mulkin jam'iyyar APC da sulhunta jiga-jigan jam'iyyar.
Asali: Legit.ng