Yanzu: Shugaba Bola Tinubu Ya Yi Sabin Nade-Nade 2 Masu Muhimmanci
- Shugaba Bola Tinubu ya yi sabbin nadi guda biyu kari kan wadanda ya yi a kwanakin baya kimanin wata biyu bayan rantsuwar kama aiki
- Jubril Gawat, tsohon hadimin Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas, ya sanar cewa Shugaba Tinubu ya nada Olusegun Dada a matsayin mataimaki na musamman kan kafafen sada zumunta
- Bashir Ahmed, tsohon hadimin Shugaba Muhammadu Buhari, shima ya sanar cewa Shugaba Tinubu ya nada Abdulaziz Abdulaziz a matsayin mataimaki na musamman kan kafafen jaridu
Aso Rock, Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nada dan gani kashe nin jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Olusegun Dada, a matsayin mashawarci na musamman kan dandalin sada zumunta.
Shugaban kasar kuma ya nada Abdulaziz Abdulaziz a matsayin mataimaki na musamman a bangaren jaridu.
Karin bayani game da nade-naden da Tinubu ya yi
An sanar da hakan ne cikin sakon taya murna da Jubril Gawat, tsohon hadimin Gwamna Babajide Sanwo-Olu, ya fitar a ranar Litnin 10 ga watan Yuli.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya wallafa sakon ne a Twitter jim kadan bayan dawowa Shugaba Tinubu babban birnin tarayya Abuja, a ranar Litinin bayan halartar taron Shugaban kasashe na ECOWAS karo na 63 a Guinea Bissau.
A yayin da ya ke Guinea Bissau, an zabi Shugaba Tinubu a matsayin Shugaban Kungiyar Tattalin Arziki na Kasashen Afirka ta Yamma, ECOWAS, yayin taron kungiyar karo na 63.
An zabi Shugaba Tinubu a matsayin shugaban ECOWAS
Shugabannin kasashen yankin Afirka ta Yamma wato ECOWAS da suka taro a kasar Guinea Bissau don taron kungiyar karo na 63 a ranar Asabar da Lahadi, 8 da 9 ga watan Yuli sun zabi Tinubu matsayin shugaba ba tare da hamayya ba.
Zaben na Tinubu a matsayin shugaban ECOWAS na zuwa ne a kalla watanni biyu bayan an rantsar da shi a matsayin shugaban kasar Najeriya na 16 lokacin da ya karbi mulki daga tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.
Ana fatan Tinubu zai fitar da sunayen ministocinsa kafin ko ranar 28 ga watan Yuli, lokacin da zai cika kwana 60 a ofis bisa yadda doka ta tanada.
Karanta sakon na Twitter a nan:
Tinubu Ya Tura Sunayen Sabbin Hafsoshin Tsaro Zuwa Majalisa
A wani rahoton kun ji cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya rubuta wasika ga Majalisar Tarayya, inda ya sanar da su cewa ya yi sabbin naɗe-naɗe.
The Nation ta rahoto cewa shugaban kasan ya tura sunayen sabbin hafsoshin tsaron da ya nada yana bukatan majalisun su tantance tare da tabbatar da su.
Asali: Legit.ng