"Ta Tabbata": Gwamnan PDP Mai Karfin Fada A Ji Ya Samu Shiga Jerin Ministocin Tinubu
- Ya tabbata cewa tsohon gwamnan jihar Enugu, Ifeanyi Ugwuanyi zai kasance cikin jerin ministocin da Bola Tinubu zai sanar
- A watan Faburairu, Ugwuanyi ya rasa kujerar neman takarar sanata a mazabar Enugu ta Arewa ga dan jam’iyyar Labour, Okey Ezea
- Kafin zabe da kuma bayan zabe da aka gudanar a wannan shekara, tsohon gwamnan ya samu kyakkyawar fahimtar juna da Bola Tinubu
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Enugu – Yayin da ‘yan Najeriya ke hankoron jiran sunayen ministocin Shugaba Bola Tinubu, ana tunanin ganin ‘yan adawa da dama a cikin jerin sunayen.
Tun bayan darewa karagar mulki a ranar 29 ga watan Mayu, Tinubu ya karbi bakwancin gwamnonin jihar Enugu da Abia, Ifeanyi Ugwuanyi da Okezie Ikpeazu a jere.
Bayan haka shugaban ya gana da sauran gwamnonin jam’iyyar PDP da suka bijirewa dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar.
'Yan Jam'iyyar PDP na iya shiga jerin ministocin Tinubu
Legit.ng ta tattaro cewa duk da babu tabbacin ko tsohon gwamnan Abia, Ikpeazu zai iya fitowa a jerin sunayen, takwaransa na jihar Enugu, Ugwuanyi ya samu shiga jerin sunayen.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Duk da cewa Ugwuanyi ba dan jam’iyyar APC ba ne, amma jajircewarsa zai iya ba shi daman kasancewa cikin wadanda za a nada a gwamnatin Tinubu, cewar Vanguard.
A wani bangaren, ana ganin yadda jam’iyyar APC ta ke cikin matsala a jihar, da kuma matsalar da hakan ya jawo a zaben da ya gabata, ba da dama ga ‘yan jam’iyyar na iya hura wutar rikicin.
Ugwuanyi na iya samun damar kasancewa a gwamnatin Tinubu
An bayyana cewa barin daya daga cikin wadanda ba sa ga maciji a jam’iyyar a jihar kamar su Ugochukwu Agballah ko Adolphus Ude ka iya jefa jam’iyyar cikin mawuyacin hali fiye da yadda ta ke ciki.
The Guardian ta tattaro a ranar Litinin 10 ga watan Yuli cewa Ugwuanyi na iya kasancewa a cikin gwamnatin shugaban kasa, Bola Tinubu saboda fahimtar juna da ke tsakaninsu.
Har ila yau kokarin tsohon gwamnan jihar Enugu, Ugwuanyi na ganin ya dinke barakar da ke tsakanin ‘yan kasar lokacin da ya ke gwamnan jihar shi ma na daga cikin damar da ya ke da ita.
El-Rufai Ya Magantu Kan Kamun Ludayin Gwamnatin Tinubu
A wani labarin, tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya yabi salon mulkin Bola Tinubu.
Tsohon gwamnan ya ce bisa ga matakan da Bola Tinubu ya dauka a kankanin lokaci ya tabbata ya kama hanya mai kyau.
Ya ce lokaci ya yi da za a ake nada mukamai bisa kwarewa a gwamnatoci ba wai wa ka sani ba.
Asali: Legit.ng