Jerin Sunaye: Tsaffin Gwamnoni 6 Da Aka Rahoto Sunansu Na Cikin Ministocin Tinubu

Jerin Sunaye: Tsaffin Gwamnoni 6 Da Aka Rahoto Sunansu Na Cikin Ministocin Tinubu

  • 'Yan Najeriya na dai ci gaba da dakon jiran ministocin da Shugaban ƙasa Bila Ahmed Tinubu zai naɗa
  • Kwanaki 18 kacal ne suka ragewa a cikin kwanaki 60 da kundin tsarin mulki ya ba shi damar aika sunayen ministocinsa ga Majalisar Dattawa
  • Majalisar zartaswar Shugaba Tinubu za ta ƙunshi ministoci 42 da masu ba da shawara na musamman 20, kamar yadda bayanai suka nuna

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Birnin tarayya, Abuja - Aƙalla tsofaffin gwamnoni shida ne ake sa ran sunayensu na cikin jerin sunayen da Tinubu zai gabatar a gaban Majalisar Dattawa domin tantancesu daga yanzu zuwa mako mai zuwa.

Shugaba Tinubu zaɓi ministocinsa daga manyan jam’iyyun ƙasar nan biyu, wato daga jam’iyyar APC mai mulki, da kuma jam'iyyar adawa ta PDP.

Ana kuma hasashen cewa Tinubu zai gauraya da masana a cikin majalisar ministocin nasa kamar yadda The Guardian ta wallafa ranar Litinin, 10 ga watan Yuli.

Kara karanta wannan

Shehu Sani Ya Fadawa Tinubu Manyan Abubuwa 2 Da Ya Kamata Ya Guji Aikatawa a Gwamnatinsa

Tsaffin gwamnoni 6 ne ake sa ran Tinubu zai ba mukaman ministoci
Tinubu zai ba El-Rufai, Ganduje, Badaru da wasu tsaffin gwamnoni 3 mukaman ministoci a gwamnatinsa. Hoto: Mohammed Badaru Abubakar, Dr. Zainab Shinkafi Bagudu, Nyesom Ezenwo Wike, Nasir El-Rufai
Asali: Facebook

Yadda majalisar zartaswar Shugaba Tinubu za ta kasance

Sabuwar majalisar zartaswar kamar yadda bayani ya nuna, za ta ƙunshi ministoci 42 da masu ba da shawara na musamman 20.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu daga cikin tsoffin gwamnonin da ka iya kasancewa cikin jerin sunayen da za a miƙawa Majalisar Dattawa sun haɗa da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai.

Sauran sun haɗa da Muhammad Badaru Abubakar tsohon gwamnan Jigawa, Abubakar Atiku Bagudu na Kebbi, Abdullahi Ganduje na Kano, da Nyesom Wike na Ribas.

An kuma tattaro cewa tsohon gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, na iya samun ministan harkokin waje. Shi ne ya riƙe ministan tama da karafa a gwamnatin da ta gabata.

A satin da ya gabata ne mai bai wa shugaba Tinubu shawara kan ayyuka na musamman, Dele Alake, ya bayyana cewa har yanzu shugaban bai fitar da sunayen ministocinsa ba.

Kara karanta wannan

Babban Jigon PDP Ya Gana da Shugaba Tinubu a Villa, Ya Yi Magana Kan Sauya Sheƙa Zuwa APC

The Cable ta ruwaito Alake na cewa da zarar Tinubu ya gama zaɓar ministocin nasa, zai bayyanawa duniya su.

Gwamnoni 6 da ake sa ran Tinubu zai naɗa ministoci

Tsofaffin gwamnonin Najeriya shida da ake kyautata zaton cewa Tinubu zai ba su muƙamin ministoci su ne:

1. Nasir El-Rufai, tsohon gwamnan jihar Kaduna

2. Abdullahi Umar Ganduje, tsohon gwamnan jihar Kano

3. Abubakar Atiku Bagudu, tsohon gwamnan jihar Kebbi

4. Mohammed Badaru Abubakar, tsohon gwamnan jihar Jigawa

5. Nyesom Wike, tsohon gwamnan jihar Ribas

6. Kayode Fayemi, tsohon gwamnan jihar Ekiti

Gwamnatin Tarayya ta koka kan yadda aka rage shan man fetur

Legit.ng ta kawo muku wani rahoto a baya kan cewa Gwamnatin Tarayya ta koka kan yadda 'yan Najeriya suka rage shan man fetur tun bayan cire tallafi.

Gwamnatin ta bayyana cewa shan man ya ragu da kaso mai yawa a yanzu idan aka yi la'akari da yadda ake sha a farkon shekarar 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng