Aisha Binani Ta Sake Kai Hukumar INEC Kara a Gaban Kotu

Aisha Binani Ta Sake Kai Hukumar INEC Kara a Gaban Kotu

  • Aisha Dahiru Binani ba ta haƙura ba da rashin nasarar da ta yi a zaɓen gwamnan jihar Adamawa da ya gabata
  • Ƴar takarar gwamnan ta jam'iyyar APC ta sake kai hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ƙara a gaban kotu
  • Binani ta sake kai ƙarar hukumar kotu ne saboda sokee bayyanata a matsayin wacce ta lashe zaɓen gwamnan jihar

FCT, Abuja - Ƴar takarar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a zaɓen gwamnan jihar Adamawa, Aisha Dahiru Binani, ta sake kai hukumar shirya zaɓe ta INEC ƙara gaban kotu.

Jaridar Vanguard tace Aisha Binani ta sake kai hukumar zaɓen ƙara kotu ne saboda soke sanar da ita da aka yi a matsayin wacce ta lashe zaɓen gwamnan jihar na ranar 18 ga watan Maris 2023.

Kara karanta wannan

Kungiyar MURIC Ta Zargi Babban Gwamnan PDP Da Yi Wa Kungiyar Kiristocin Najeriya Aiki

Aisha Binani ta sake kai INEC kara gaban kotu
Aishatu Dahiru Binani, 'yar takarar gwamnan jihar Adamawa ta jam'iyyar APC
Asali: UGC

Binani, ta hannun lauyanta Miichael Aondoaka, SAN, ta shigar da sabuwar ƙarar ne a gaban mai shari'a Donatus Okorowo na babbar kotun tarayya da ke birnin tarayya Abuja.

A cikin ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/935/2023, ƴar takarar ta jam'iyyar APC a zaɓen, tana ƙarar hukumar INEC, jam'iyyar PDP da ɗan takararta gwamna Ahmadu Fintiri.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin Binani na sake kai ƙara kotu

Binani, tana son kotun ta sake duba matakin INEC na warware bayyanata a matsayin wacce ta lashe zaɓen da Hudu Yunusa-Ari ya yi tun da farko, cewar rahoton The Guardian.

Aondoaka ya yin gabatar da ƙarar a ranar Litinin, ya bayyana cewa kotun sauraron ƙararrakin zaɓe ce ke da hurumin yin hukunci kan wacce yake wakilta bisa tanadin sashi na 149 na sabuwar dokar zaɓe ta shekarar 2022.

Ya bayyana cewa hukuncin na INEC ya hana Binani amfanuwa da sashi 285(6) wanda ya yi tanadin kwanaki 180 waɗanda a cikinsu za a yi hukunci kan ƙarar da ta kai a gaban kotun zaɓen a ranar 6 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

Dakarun Sojoji Sun Yi Galaba Kan 'Yan Ta'adda Sun Ceto Mutane Masu Yawa Da Suka Sace a Jihar Arewa

INEC Na Tuhumar Hudu Ari

A wani labarin na daban kuma, hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta gabatat da tuhume-tuhumen da ta ke yi wa dakataccen kwamishinan zaɓen jihar Adamawa.

Hukumar INEC na tuhumar Hudu Yunusa-Ari da aikata laifuka shida kan rawar da ya taka a dambarwar zaɓen gwamnan jihar Adamawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng