Tsohon Dan Takarar Gwamnan Edo Ya Sauya Sheka Daga PDP Zuwa APC
- Tsohon ɗan takarar gwamnan Edo a inuwar PDP, Gideon Ikhine, ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC
- Ya tabbatar da haka ranar Lahadi bayan tura takardar fita daga PDP zuwa shugaban jam'iyya na gundumarsa
- Ya ce rigimgimun cikin gida a PDP ne suka tilasta masa sauya sheka zuwa APC domin samun damar yi wa mutanensa a aiki
Edo State - Mataimakin darakta janar na kwamitin yaƙin neman tazarcen gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo a zaben 2020, Injiniya Gideon Ikhine, ya fice daga jam'iyyar APC.
Jaridar Punch ta tattaro cewa babban jigon siyasan ya sauya sheka zuwa jam'iyar APC ne jim kaɗan bayan barin PDP.
Ya tabbatar da wannan matakin a wasiƙar murbus daga kasancewa mamba da ya aike wa shugabaan PDP na gunduma ta 7 (Ukpenu/ Ujolen/ Emuhi) Ekpoma, ƙaramar hukumar Esan ra yamma a Edo.
Bata-Gari Sun Kai Farmaki Kan Sakatariyar Jam'iyyar SDP a Jihar Kogi, Sun Barnata Dukiya Mai Tarin Yawa
Takardar mai ɗauke da kwanan watan 8 ga watan Yuli, 2023 ta shiga hannun 'yan jarida ranar Lahadi, 9 ga watan Yuli.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Injiniya Ikhine ya bayyana cewa yana alfahari da ɗumbin gudummuwar da ya bayar wajen gina jam'iyyar PDP a tsawon shekaru 24 da suka gabata.
A takardar, tsohon Jigon PDP ya ce:
"Ina alfari da zama ɗaya daga cikin waɗanda suka bada gudummuwa wajen kawo ci gaba da nasararu a PDP tsawon shekaru, PDP ta samu sakamako mai kyau a gundumata shekaru 24 da muka yi aiki tare."
"Har yanzu kudiri na ga al'ummar gunduma ta 7, ƙaramar hukumar Esan bai sauya ba kuma zan ci gaba da kokarin inganta rayuwarsu a duk inda na tsinci kaina."
Meyasa ya fita daga PDP zuwa APC?
Da yake bayyana dalilinsa ranar Lahadi, Mista Ikhine ya ce babban abinda ya sa ya ga haka ya dace ya yi shi ne rigingimun da suka hana PDP zaman lafiya, tawagar Obaseki ta maida hankali wajen yaƙar mutanen kirki.
A rahoton This Day, jigon siyasan ya ƙara da cewa:
"Ricikin cikin gida a PDP ne babban dalilin sauya sheƙar da na yi saboda bana hangen zan cika buri na a daidai lokacin da Obaseki ke takun saƙa da tawagar Legacy."
"Na ɗauki kaso 30 cikin 100 na mambobin PDP mun koma jam'iyyar APC. Dama na yi wa APC aiki a zaɓen da ya shuɗe saboda rashin adalcin da aka mun a zaɓen Esan."
Gwamnan Neja Ya Kori Ma'aikata da Dukkan Hadiman Magabacinsa Nan Take
A wani labarin na daban kuma Gwamnan Neja, Umar Bago, ya kori hadiman da magabacinsa ya naɗa a muƙamai daban-daban gabanin ranar 29 ga watan Mayu
A wata sanarwa da ofishin SSG ya fitar, gwamnan ya kuma sallami baki ɗaya mambobin majalisun gudanarwa na hukumomin gwamnati.
Asali: Legit.ng