MURIC Ta Zargi Gwamna Adeleke Na Jihar Osun Da Yi Wa Kungiyar CAN Aiki
- Kungiyar kare haƙƙin Musulmi (MURIC), ta caccaki gwamnan jihar Osun kan nunawa Musulmi banbanci
- Daraktan ƙungiyar ta MURIC, Farfesa Ishaq Akintola ne ya bayyana hakan a ranar Litinin
- Akintola ya zargi Gwamna Ademola Adeleke, da yi wa ƙungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) aiki ta ƙarƙashin ƙasa
Osun - Ƙungiyar kare haƙƙin Musulmi (MURIC), ta caccaki jerin sunayen kwamishinonin da gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke ya fitar.
A ranar Juma’a, Majalisar Dokokin jihar Osun, ta karɓi jerin sunayen waɗanda Gwamna Adeleke ke son naɗawa kwamishinoni da masu ba da shawara na musamman.
Jerin sunayen dai na zuwa ne bayan watanni bakwai da rantsar da shi a kan karagar mulki kamar yadda The Cable ta wallafa.
Mutane 25 ne Gwamna Adeleke zai bai wa muƙami
Mutane 25 ne gwamnan ya gabatar da sunayen nasu, wanda daga ciki akwai mambobi biyu na tsohon gwamnan jihar, Rauf Aregbesola, Kolapo Alimi da Biyi Odunlade.
Wata Sabuwa: Aisha Binani Ta Sake Kai Hukumar INEC Kara Gaban Kotu Kan Zaben Gwamnan Adamawa, Ta Fadi Bukatarta
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A wata sanarwa da Farfesa Ishaq Akintola, babban daraktan MURIC ya fitar ranar Litinin, ya ce jerin sunayen waɗanda Adeleke ya gabatar, ya ƙunshi Musulmai bakwai da Kiristoci goma sha bakwai.
Kungiyar ta zargi gwamnan jihar Osun da nuna wariya da kuma tauye haƙƙin Musulmin jihar.
Wani ɓangare na sanarwar na cewa:
"Mun yi Allah wadai da wannan danne muƙamin da ya kamata ace Musulmai ne aka bai wa."
Farfesa Ishaq ya zargi Adeleke da yaudara da kuma yi wa kungiyar CAN aiki
Farfesa Ishaq Akintola ya kuma zargi gwamnan jihar ta Osun Ademola Adeleke da yaudarar Musulmin jihar da nuna cewa shi Musulmi ne.
Ya ce Adeleke mamba ƙungiyar kiristocin Najeriya (CAN) ne, kuma yana yi mata aiki ne ta ƙarƙashin ƙasa.
Akintola ya ƙara da cewa babban burin Adeleke shi ne ya zalunci Musulmin jihar ta Osun, kuma yanzu ga dama ya samu tunda ya zama gwamna.
Premium Times ta ruwaito cewa, mutane 25 ne Adeleke yake son bai wa kwamishinoni, da wasu 25 da yake son bai wa muƙamin masu ba da shawara na musamman.
Muric ta ce za ta barranta da 'yan siyasa Musulmi da basu amfani Musulunci ba
Legit.ng a kwanakin baya ta kawo muku wani rahoto inda kungiyar kare hakkin Musulmi (MURIC), ta bayyana cewa za ta barranta da duk wani ɗan siyasa Musulmi da bai amfani Musuluncin ba.
Daraktan ƙungiyar, Farfesa Ishaq Akintola ne ya bayyana haka a yayin da yake Allah wadai da irin ɗabi'un tsohon gwamnan jihar Osun, Rauf Aregbesola.
Asali: Legit.ng