Gwamnan Neja Ya Kori Dukkan Hadiman da Tsohon Gwamna Ya Nada

Gwamnan Neja Ya Kori Dukkan Hadiman da Tsohon Gwamna Ya Nada

  • Gwamnan Neja, Umar Bago, ya kori hadiman da magabacinsa ya naɗa a muƙamai daban-daban gabanin ranar 29 ga watan Mayu
  • A wata sanarwa da ofishin SSG ya fitar, gwamnan ya kuma sallami baki ɗaya mambobin majalisun gudanarwa na hukumomin gwamnati
  • Bayan yaba musu bisa kokarin da suka yi, mai girma gwamna ya umarci su aje kayan gwamnati su bar ofis nan take

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Niger state - Gwamnan jihar Neja, Umar Bago ya rushe baki ɗaya majalisun gudanarwa na hukumomin gwamnati wanda magabacin ya naɗa a lokacin mulkinsa.

Rahoton Daily Trust ya tattaro cewa baya ga haka, gwamna Bago ya kori baki ɗaya hadiman da tsohon gwamna Abubakar Sani Bello ya naɗa gabanin ranar rantsuwa 29 ga watan Mayu, 2023.

Gwamna Muhammad Umar Bago na jihar Neja.
Gwamnan Neja Ya Kori Dukkan Hadiman da Tsohon Gwamna Ya Nada Hoto: Umar Bago Media Centre
Asali: Facebook

Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Neja (SSG), Alhaji Abubakar Usman, ya fitar ranar Litinin, 10 ga watan Yuli, 2023.

Kara karanta wannan

Zance Ya Ƙare: Kwamitin Binciken da Gwamna Ya Kafa Ya Gano Gaskiya Kan Ɗalibar Da Ake Zargi da Ƙara Makin JAMB

SSG ya bayyana cewa gwamna Umar Bago ya bada umarnin sallama da kuma soke naɗe-naɗen hadiman nan take babu ɓata lokaci.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Alhaji Usman ya ƙara da bayanin cewa korar ta shafi mambobin majalisun gudanarwan hukumomi masu wa'adi da marasa wa'adi kuma ya roƙi su gaggauta barin Ofis nan take.

Haka zalika ya yaba wa baki ɗaya hadimai da sauran ma'aikatan da matakin ya shafa bisa ɗumbin gudummuwar da suka bayar wajen bunƙasa jihar da tafiyar da Ofisoshinsu.

Ya umarci mutanen da su miƙa duk wata kadarori gwamnati wanda ya ƙunshi motoci da sauransu ga babban daraktan hukumomin da suka jagoranta kafin yau.

Gwamna Bago ya musu fatan alheri

Sanarwan tana ɗauke da sa hannun mai magana da yawun ofishin sakataren gwamnatin Neja, Lawal Tanko, rahoton Solabace ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Mataimakin Shugaban Ƙasa Ya Yi Kus-Kus da Wasu Jiga-Jigai a Aso Villa, Ya Roƙi Alfarma 1 Tal

Gwamna Bago ya yi wa daukacin hadimai da mambobin majalisun gudanarwa na hukumomin gwamnati fatan alheri a dukkan al'amuran da suka sanya a gaba.

Mataimakin Shugaban Kasa Ya Gana Da Tsoffin Sanatoci a Villa, Ya Roki Abu 1

A wani labarin na daban kuma Kashim Shettima ya karbi bakunci wakilan mambobin majalisar dattawa ta 9 da ta gabata a fadar shugaban kasa.

Bayan kammala ganawar, shugaban tawagar sanatocin ya bayyana manyan dalilin da ya sa suka ziyarci mataimakin shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262