Saura Ƙiris: Tinubu Ya Aikawa EFCC Da DSS Sunayen Waɗanda Za Su Zama Ministoci

Saura Ƙiris: Tinubu Ya Aikawa EFCC Da DSS Sunayen Waɗanda Za Su Zama Ministoci

  • Da alama ba da dadewa ba za a san su wanene Bola Ahmed Tinubu zai zaba a matsayin Ministocinsa
  • Majiyoyi sun tabbatar da cewa sunayen sun kusa fitowa, har an fara yin bincike a kansu a EFCC da DSS
  • Ana sa ran da zarar an karkare binciken nan, a aikawa Majalisar dattawa jerin wadanda za su tantance

Abuja – Yayin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya shafe kwanaki 40 a ofis, jama’a sun kai bango wajen sauraron wadanda za a zaba su zama Ministoci.

A rahoton da Punch ta fitar a ranar Litinin, an samu labari ‘yan majalisa sun fara damuwa kan abin da ya hana aiko sunayen wadanda za a ba Minista.

Wasu Sanatoci da su ka yi magana ba tare da bari an kama sunayensu ba, sun ce ba su tunanin za a cigaba da bata lokaci kafin a fitar da Ministocin kasar.

Kara karanta wannan

Kwanaki 42 Akan Mulki, Gwamnatin Tinubu Ta Gagara Cika Babban Alkawari Da Ta Dauka Wa Yan Najeriya

Tinubu
Bola Tinubu bai nada Ministoci ba Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Sunayen ya kai teburin EFCC da DSS

Majiya ta shaidawa jaridar cewa jami’an EFCC da DSS da sauran hukumomin tsaro su na daf da kammala binciken wadanda ake sa ran su rike mukamin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hukumar DSS ta fararen kaya da na hannun-daman shugaban kasan su na tantance wadanda aka zaba kafin a fitar da sunayensu zuwa ga majalisar dokoki.

Tsohon ‘dan majalisar tarayya, Hon. Alex Egbona ya ce dole ne a sanar da Ministoci cikin watanni biyu, ya na sa ran ba zai wuce makon yau zuwa gobe be.

Shawarwarin da ake ba Gwamnati

‘Dan majalisar Ideato, Hon, Ugochinyere Ikenga ya ce an kusa sanar da sababbin Ministoci.

Akwai irinsu Uche Nwosu da ke ganin babu laifi a dauko ‘Yan Najeriya da ke kasashen waje a ba su kujerar domin nemo wadanda su ka san kan aiki.

Kara karanta wannan

Hukumar NDLEA Tayi Kamen Masu Harkar Kwayoyi, An Yi Ram da Malaman Addini

Hadimin Atiku Abubakar, Demola Olarewaju ya ce shugaban kasan ba zai iya dauko wadanda su ka san aiki ba, domin dole ya yi wa ‘yan siyasa sakayya.

Ita kuwa wakiliyar mata a kungiyar ECOWAS, Beatrice Eyong ta na so shugaba Bola Tinubu ya warewa mata 50% na duk mukaman da zai raba a mulkinsa.

Idan an tashi rabon mukaman, jaridar Tribune ta ce majalisar wakilai ta bukaci gwamnatin tarayya ta ware ko da 10% na mukamai domin masu nakasa.

Ana rade-radin cewa a gwamnatin nan, masu ba shugaban kasa shawara za su samu karfi sosai.

Ayodele Fayose zai zama Minista?

A rahoton da mu ka fitar a farkon makon nan, an ji Ayodele Fayose ya fadi dalilinsa na marawa Bola Tinubu baya kan PDP, kuma ya ce ba ya neman Minista.

Fayose yake cewa duk wanda ya kai shekara 65 a Duniya, kamata ya yi Bola Tinubu ya fada masa ya kawo ‘ya ‘yansa a ba shi mukami, domin shi ya tsufa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng