Bata-Gari Sun Farmaki Sakatariyar Jam'iyyar SDP a Jihar Kogi
- Wasu miyagun ɓata-gari sun dira a sakatariyar jam'iyyar Social Democratic Party (SDP) a jihar Kogi inda suka tafka ta'asa
- Ɓata-garin sun lalata wani ɓangare na sakatariyar tare da bankawa wasu kayayyaki wuta ba gaira ba dalili
- Ɗan takarar mataimakin gwamnan jihar na jam'iyyar ya nuna takaicinsa kan wannan aika-aika da ɓata-garin suka tafka musu
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Kogi - Ɓata-gari sun lalata sakatariyar jam'iyyar Social Democratic Party (SDP) da ke akan shatatalen Paparanda a birnin Lokoja, babban birnin jihar Kogi.
Jaridar The Punch ta kawo rahoto cewa wani sassan sakatariyar an lalata shi sannan an ƙona wasu kayayyaki da misalin ƙarfe 10:15 na safiyar ranar Lahadi amma babu rahoton yin asarar rai.
Babban jigo a jam'iyyar SDP ya yi Allah wadai da harin
Ɗan takarar mataimakin gwamnan jam'iyyar SDP na jihar, Mr Sam Abenemi, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ga manema labarai ranar Lahadi a birnin Lokoja, ya bayyana harin a matsayin abun takaici wanda bai dace ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Abenemi ya bayyana cewa ya kaɗu matuƙa kan hanyar da yaƙin neman zaɓen gwamnan jihar na watan Nuwamba ta ke bi.
A kalamansa:
"A sani na yaƙin neman zaɓe kawai nemo ƙuri'u ake yi, amma hanyar da wannan takarar ke bi abun tsoro ce abun takaici."
"Yau da safen nan da misalin ƙarfe 10:15, wasu ɓata-gari waɗanda mu ke zargin ɗaukar nauyinsu aka yi sun dira a sakatariyar jam'iyyarmu a Lokoja, suka lalata ta sannan suka ƙona wasu kayayyakin."
"Wannan shaiɗanci ne abun takaici wanda bai dace ba. Ba haka ake siyasa ba a ƙasa mai dimokuraɗiyya irin ta mu."
Ɗan takarar mataimakin gwamnan ya kuma yi kira ga jami'an tsaro da ke a jihar da su cafko ɓata-garin da suka kai farmakin kan sakatariyar jam'iyyar, cewar rahoton Vanguard.
Jam'iyyar SDP Ta Bankado Sirrin Yahaya Bello
A wani labarin na daban kuma, jam'iyyar SDP a jihar Kogi ta bayyana cewa tana da faifan bidiyon gwamnan jihar, Yahaya Bello, yana iƙirarin cewa ya gwanance wajen iya harbi.
Hakan na zuwa ne dai bayan ɓangarorin biyu sun yi musayar kalamai kan harin da aka kai kan tawagar ɗan takarar gwamnan jam'iyyar SDP, Muritala Yakubu Ajaka.
Asali: Legit.ng