Shugaba Tinubu Ya Gana da Tsohon Gwamnan Ekiti, Ayo Fayose a Aso Villa
- Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose, ya gana da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a Aso Rock ranar Alhamis, 6 ga watan Yuli
- Hadimin shugaban kasa ne ya tabbatar da haka a shafin Tuwita kuma ya wallafa Hotunan Tinubu tare da Ayo Fayose a Villa
- A jawabinsa bayan gana wa da shugaban kasa, Fayose ya jaddada cewa ba bu wani shirin zai fice daga jam'iyyar PDP zuwa APC mai mulki
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu (GCFR) ya karɓi bakuncin tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose a fadar shugaban kasa da ke Abuja ranar Alhamis.
Hadimin shugaban kasa na fannin sadarwan zamani da dabaru, Daddy D.O ne ya tabbatar da haka a shafinsa na tuwita duk da bai bayyana abinda suka tattauna ba.
Haka nan kuma mamban jam'iyyar APCn ya wallafa Hotunan Bola Tinubu yana murmushi tare da Fayose a fadar shugaban kasa yau 6 ga watan Yuli, 2023.
Shin yana shirin sauya sheƙa ne daga PDP zuwa APC?
Vanguard ta rahoto cewa jim kaɗan bayan ganawar, Fayose ya ce ba zai yi wata-wata ba zai fara caccakar shugaba Tinubu da zaran ya karya alkawurran da ya ɗauka lokacin kamfe.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon gwamman ya ƙara da tabbatar da cewa ba zai taɓa barin jam'iyyar PDP don kawai ya koma inuwar jam'iyyar All Progressive Congress (APC) ba.
Legit.ng Hausa ta tattaro cewa Fayose na ɗaya daga cikin mutanen da suka buƙaci Tinubu ya yi maganin tsirarun mutane da suka fake suna amfana da kuɗin tallafin mai.
Kwana 2 bayan ya karbi mulki 31 ga watan Mayu, Fayose ya ce shugaba Tinubu ba boka bane amma zai iya haɗa kai da tawagarsa su bullo da dubarun saita akalar ƙasar nan.
Shugaba Tinubu Ya Tura Sunayen Sabbin Hafsoshin Tsaro Zuwa Majalisa
A wani rahoton na daban kun ji cewa Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya buƙaci majalisar tarayya ta tabbatar da hafsoshin tsaron da ya naɗa kwanakin baya a hukumance.
A wata wasiƙa mai ɗauke da adireshin kakakin majalisar wakilan tarayya, shugaban ƙasa ya roƙi 'yan majalisun su hanzarta tabbatar da naɗin babban hafsan tsaro (CDS) da sauran hafsoshi.
Asali: Legit.ng