Kano: Jam'iyyar APC Ta Bukaci Ganduje Ya Yi Fatali da Gayyatar Hukumar Cin Hanci
- Jam'iyyar APC reshen jihar Kano ta yi fatali da gayyatar da hukumar yaƙi da cin hanci ta tura wa tsohon gwamna Abdullahi Ganduje
- A wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun shugaban APC da sakatare, jam'iyyar ta buƙaci Ganduje kar ya amsa gayyatar
- Ta ƙara da cewa gwamnatin Kano ta dawo da batun bidiyon dala ne domin ɓata wa Ganduje suna a idon Tinubu
Kano - Jam'iyyar APC reshen jihar Kano ta tsoma baki kan dambarwan bidiyon daloli na tsohon gwamna, Dakta Abdullahi Umar Ganduje.
Daily Trust ta ruwaito cewa APC ta buƙaci tsohon gwamnan kar ya amsa gayyatar da hukumar yaƙi da cin hanci ta jihar Kano (PCACC) ta aiko masa.
Idan baku manta ba a cikin shirin Channels tv, shugaban hukumar, Muhuyi Magaji Rimingado, ya ce sun gayyaci Ganduje domin ya yi ƙarin haske kan bidiyon dala a mako mai zuwa.
Amma da suke martani kan lamarin, shugaban APC na Kano, Abdullahi Abbas da sakararen jam'iyya na jiha, Alhaji Zakari Sarina, sun zargi gwamnatin Kano da ƙulla wa Ganduje makirci.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Abdullahi Abbas da Zakari Sirina, APC ta ce:
"Mun fahimci NNPP ta dawo da batun badaƙalar bidiyon dala ɗanye ba don komai ba sai don ɓata wa Ganduje suna, kowa ya san lamarin nan siyasa ce kuma yana gaban Kotu."
"Makamancin irin haka aka yi da nufin ruguza yunƙurin tsohon gwamnan ya gaza samun tikitin takarar gwamna a babban zaben 2019."
"A wannan karon, sun dawo da batun ne da nufin haddasa rikici tsakanin shugaban ƙasa, Bola Tinubu da Ganduje, wanda yana ɗaya daga cikin na hannun daman Tinubu a arewa."
Jam'iyyar APC ta ƙara da cewa gudummuwar da Ganduje ya bai wa tafiyar Tinubu tun daga zaɓen fidda gwani har zuwa cin babban zaɓe ba zata canja ba kuma yana shan yabo kan haka.
Sanarwan ta ce kyakkyawar dangantakar da ke tsakanin shugaban ƙasa da Ganduje na nan ta karfinta kuma babu mai iya ruguza wannan alaƙa.
Shugaba Tinubu Zai Sanar da Sabuwar Ranar Kidaya a Najeriya
A wani labarin kuma Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu , zai sanar da sabuwar ranar da za'a gudanar da ƙidayar al'umma da gidaje a Najeriya.
Shugaban hukumar kidaya ta ƙasa (NPC), Nasir Kwarra, shi ne ya bayyana haka ga masu ɗauko labaran gidan gwamnati ranar Alhamis a Abuja.
Asali: Legit.ng