Yanzu Yanzu: INEC Na Tuhumar Dakataccen Kwashinan Zaben Adamawa Kan Laifuka 6
- Za a fara shari’ar Hudu Yunusa-Ari da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta a ranar 12 ga watan Yuli
- Hukumar INEC ta gabatar da tuhume-tuhume shida a kan dakataccen kwamishina zaben jihar Adamawa
- Ari dai ya shiga matsala ne tun bayan da ya ayyana Aisha Binani a matsayin wacce ta lashe zaben Adamawa tun ba a kammala tattara sakamako ba
Adamawa - Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta gabatar da tuhume-tuhume shida a kan kwamishinan zaben Adamawa, Hudu Yunusa-Ari, wanda hukumar ta dakatar yayin zaben gwamnan jihar na ranar 18 ga watan Maris.
Jaridar The Cable ta rahoto cewa an gabatar da tuhume-tuhumen ne a gaban babbar kotu da ke Yola, babban birnin jihar Adamawa.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hukumar INEC ta saki a ranar Alhamis, 6 ga watan Yuli, tana mai cewa hukumar ta sake duba takardar kara daga hannun yan sanda, sannan ta kafa hujja a kan dakataccen kwamishinan.
Ku tuna cewa rundunar yan sandan Najeriya sun kama Yunusa-Ari kan zaben gwamnan da dakataccen kwamishinan ya jagoranta a jihar Adamawa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Sai dai kuma, an bayar da belinsa sannan aka bukaci ya dunga gabatar da kansa a hedkwatar rundunar yan sanda dun ranar mako.
Za a fara sauraron shari'ar a ranar 12 ga watan Yuli, INEC
A cikin sanarwar da ta fitar, hukumar zaben ta bayyana cewa kotun ta sanya ranar 12 ga watan Yulin 2023 domin fara sauraron shari’ar, rahoton Leadership.
Takaddamar da aka sha a zaben gwamnan Adamawa
Yunusa-Ari ya haddasa takaddama a zaben gwamnan jihar Adamawa inda ya ayyana Aisha Binani Dahiru ta jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a matsayin wacce ta lashe zaben Adamawa tun ba a kammala tattara sakamakon zaben ba.
Hukumar INEC ta sanar da soke sanarwar da ya yi sannan ta aika sammaci ga dakataccen kwamishinan zaben a hedkwatarta da ke Abuja.
Daga bisani, hukumar zaben ta rubuta wasika ga yan sanda inda ta nemi su hukunta Yunusa-Ari a kan laifin magudin zabe.
A ranar 20 ga watan Afrilu ne tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da dakatar da kwamishinan zaben na Adamawa har sai yan sanda sun kammala bincike.
Bayan kwana daya da haka, sai INEC ta ce ba ta san inda Yunusa-Ari ya shiga ba.
Hakazalika, Hudu ya ce babu wanda ya ba shi kudi don ya ayyana Binani a matsayin wacce ta lashe zabe, sannan ya ce shi bai shiga yar buya ba.
Mun kasa hukunta dakataccen kwamishinan zaben Adamawa, INEC
A baya mun ji cewa hukumar zabe ta bayyana cewa tana gab da daukar mataki a kan dakataccen kwamishinan zaben Adamawa, Hudu Ari.
Kwamishinan yaɗa labarai da ilimantar da masu kaɗa kuri'a na INEC ta ƙasa, Festus Okoye ne ya bayyana haka.
Asali: Legit.ng