An Karrama Tinubu Yayin Da Masu Adaidaita Sahu Suka Shafe Kilomita 757 Daga Lagos Zuwa Abuja, Sun Fadi Bukatu

An Karrama Tinubu Yayin Da Masu Adaidaita Sahu Suka Shafe Kilomita 757 Daga Lagos Zuwa Abuja, Sun Fadi Bukatu

  • Kungiyar Masu Adaidaita Sahu a Najeriya (TOAN) sun kwashi jiki daga Lagos zuwa Abuja a adaidaita sahun don yin mubaya’a ga Shugaba Tinubu
  • Shugaban kungiyar reshen Ajah shi ya sanar da haka ga ‘yan jaridu a ranar Laraba 5 ga watan Yuli inda ya ce sun yi tafiyar kilomita 757
  • Ya ce musabbabin tafiyar shi ne don nuna goyon baya ga sabuwar gwamnati da kuma neman taimako ga matasa musamman masu adaidaita sahu

FCT, Abuja – Masu adaidaita sahu karkashin Kungiyar Masu Adaidaita Sahu ta Najeria (TOAN) sun isa birnin Abuja don karrama Shugaba Bola Tinubu.

Masu adaidaita sahun sun iso Abuja ne bayan tafiyar kilomita 757 daga jihar Lagos har birnin Tarayya don nuna goyon bayansu ga shugaban da kuma gwamnatinsa.

Kara karanta wannan

Asalin Abin da Ya Kai Ni Wajen Tinubu a Aso Rock – ‘Dan Takaran Shugaban Kasa a PDP

Masu Adaidaita Sahu Sun Shafe Kilomita 757 Daga Lagos Zuwa Abuja Don Tinubu
Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu. Hoto: Twitter.
Asali: Twitter

A wata hira da Daily Trust, shugaban kungiyar reshen Ajah, Babatunde Olisah ya ce ziyarar an yi ta ne don taya shugaban murnan cika kwanaki 38 a karagar mulki.

Masu adaidaita sahun sun nemi alfarma a wurin Tinubu

Ya ce bayan haka sun nemi gudumawar gwamnati da goyon bayanta ga matasa musamman masu adaidaita sahu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewarsa:

“Da ni abokan aiki na Akintade Temitope da Ahmed Bolaji mun sayi sabbin adaidaita sahu don gudanar da wannan tafiya.
“Mun yi tafiyar kilomita 757 daga jihar Lagos zuwa Abuja mai tsawon sa’o’i 17 akan hanya don nuna goyon baya ga shugaban kasa da kuma neman taimako ga matasa musamman ‘yan kungiyarmu.
“Mun kasha kudaden da suka kai N100,000 na man fetur akan adaidaita sahu guda biyu mun tsaya a Ijebu Ode a Akure kafin ci gaba da tafiya zuwa Abuja don yabawa Tinubu da neman taimako ga matasa.”

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Shugaba Tinubu Ya Sa Labule da Wasu Manyan Jiga-Jigan PDP 2 a Aso Villa

Olisah ya ce 'yan Najeriya sun kwallafa rai a gwamnatin Tinubu

Olisah ya ce ‘yan Najeriya sun kwallafa rai sosai a mulkin Tinubu ya ce sun tabbatar da hakan yayin tafiya daga Lagos zuwa Abuja yadda mutane suke nuna musu goyon bayan, cewar rahotanni.

Ya roki shugaban da kada ya watsawa ‘yan Najeriya kasa a ido ganin yadda suke da buri akan gwamnatinsa.

Dalilin Zuwa Na Wajen Tinubu A Fadarsa – ‘Dan Takaran Shugaban Kasa A PDP

A wani labarin, jigo a jam'iyyar PDP, Anyim Pius Anyim ya bayyana dalilin zuwanshi fadar shugaban kasa.

Ziyarar ta Anyim Pius ta saka wa mutane shakku da rudani kan dalilin wannar ganawar sirri.

Anyim ya ce ya je fadar ne don taya shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu murnar cin zabe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.