Gwamnoni Sun Yi Wuf Sun Tsoma Baki a Rikicin da Ya Fara Kacalcala Jam’iyyar APC

Gwamnoni Sun Yi Wuf Sun Tsoma Baki a Rikicin da Ya Fara Kacalcala Jam’iyyar APC

  • A sakamakon sabanin da zaben shugabannin majalisa ya kawo, Gwamnonin APC sun yi zaman sasanci
  • Shugaban kungiyar PGF, Hope Uzodinma ya shaida cewa za su dinke barakar da aka samu a jam’iyya
  • A baya an ji Abdullahi Adamu ya ce babu ruwan jam’iyya da wadanda aka ba mukamai a Majalisa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Kungiyar PGF ta Gwamnonin APC ta yi alkawarin sasanta sabanin da aka samu tsakanin shugabanninta jam’iyya na kasa da majalisar tarayya.

A rahoton Punch, an samu labari Gwamnonin jam’iyyar APC su na kokarin sasanta majalisar APC NWC da shugabannin majalisar dattawa da na wakilai.

Abdullahi Adamu ya nesanta jam’iyyar APC da mutanen da Godswill Akpabio da Tajudeen Abbas su ka sanar a matsayin sababbin shugabannin majalisa.

'Yan APC
Shugabanni da Gwamnonin APC Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: UGC

Ganin NWC a karkashin jagorancin Sanata Adamu ta barranta daga aikin majalisa, Gwamnonin APC na kokarin yadda za a dinke barakar da aka samu.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaba Tinubu Ya Sa Labule da Shugaban APC Na Ƙasa da Sakatare a Villa

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Rahoton ya ce kungiyar Gwamnonin na APC ta nuna an samu akasi ne har majalisa ta sanar da shugabanninta ba tare da sanin uwar jam’iyya mai-ci ba.

Gwamna Hope Uzodinma ya yi magana

Shugaban kungiyar PGF, Hope Uzodinma ya ce za su magance sabanin cikin gidansu.

Jaridar ta rahoto Gwamna Uzodinma ya na kare Adamu, ya na cewa shugaban jam’iyyar bai nesanta kan sa da Sanata Akpabio da Rt. Hon. Abbas ba.

"Mu na da hanyoyin da mu ke bi wajen dinke barakarmu irin wannan. Gwamnonin APC da jam’iyya na tare da shugabannin majalisar tarayya.
Ba mu da wata matsala ko kadan. Mu na taya junanmu murna a kan yadda aka yi zaben majalisa, yanzu mu na da shugabanin majalisa a Najeriya."

- Hope Uzodinma

An raba kan 'Yan NWC

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Sabuwar Rigima Ta Kunno Kai a Jam'iyyar APC Kan Jagororin Majalisa

A rahoton Vanguard, an ji cewa wasu mutum uku a cikin shugabannin APC na kasa sun karyata Adamu, sun ce da saninsu majalisa ta nada shugabanni.

Wannan ya jawo irinsu Gwamna Mai Mala Buni, Umar Bago da sauran ‘yan PGF su ka zauna domin ganin babu rabuwar kai, ana tafiya da kowa a APC.

Babajide Sanwo-Olu, Yahaya Bello, Abdullahi Sule, Inuwa Yahaya, Nasir Idris da Hadiza Sabuwa Balarabe su na cikin wadanda aka yi taron nan da su.

Kotu ta kora Sanata daga APC

Rahoton da mu ka fitar a makon nan, ya nuna cewa kotun tarayya ta jikawa tsohon Gwamnan Gombe aiki, an ce ya tashi daga zama ‘Dan Jam’iyyar APC.

Shugabannin APC na Gombe sun yi nasara wajen fatattakar Sanata Mohammed Danjuma Goje daga jam’iyya. Hukuncin da kotu tayi ya ba su gaskiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng