A Karshe, Shugaba Tinubu, INEC, APC Sun Fara Kare Kansu A Kotu

A Karshe, Shugaba Tinubu, INEC, APC Sun Fara Kare Kansu A Kotu

  • Kotun sauraron karar zaben shugaban kasa ta cigaba da zamanta yayin da Shugaba Bola Tinubu zai fara kare kansa a ranar Talata, 4 ga watan Yuli
  • Hakan na zuwa ne yayin da Peter Obi na jam'iyyar Labour da Atiku Abubakar na jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, suka shigar da kararraki a kansa
  • Kazalika, Shugaba Tinubu zai kare kansa daga zargin da ke kunshe cikin rahoton tawagar masu sanya ido kan zabe na Tarayyar Turai wato EU ta yi kan zaben shugaban kasa na 2023

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai fara kare kansa a shari'ar da ake yi a kotun sauraron karar zaben shugaban kasa a ranar Talata, 4 ga watan Yuli.

Rahoto da BBC Pidgin ta fitar ya tabbatar da hakan inda aka ce Shugaba Tinubu zai fara kare kansa a matsayin mutum na biyu da aka yi kara cikin takardar da Peter Obi na jam'iyyar Labour da Atiku Abubakar na Peoples Democratic Party suka shigar na kallubalantar nasarar Tinubu a zaben shugaban kasa na ranar 25 ga Fabrairu.

Kara karanta wannan

Shugaban Kasa Bola Tinubu Ya Yanke Jiki Ya Fadi Yayin Rangadi? Gaskiya Ta Bayyana

Tinubu ya fara kare kansa a kotun zabe
Shugaba Tinubu ya fara kare kansa bisa zargin da ake masa a kotun zabe. Hoto: @OfficialABAT
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An tattaro cewa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta, INEC, ta fara kare kanta a kotun kimanin awa 24 da suka gabata.

Shaida guda daya tak aka gabatar a yayin da INEC ta fara kare kanta don a masa tambayoyi yayin da ta mika wa kotun wasu takardu a matsayin hujja.

Shaidan, Dakta Lawrence Bayode, mazaunin Abuja kuma kwararre a bangaren fasahar zamani wato ICT da ke wa INEC aiki, ya riga ya rubutta jawabinsa tun a watan Afrilu.

A bangare guda, jagoran lauyoyin INEC, Abubakar Mahmood, ya yi nuni ga sakin layi na hudu cikin rubutaccen hujjar da shaidan ya bada, bayan ya buga a takarda.

Lauyan na INEC ya gabatar da wannan hujjar da ya fitar daga na'ura a matsayin hujja ga alkalai biyar da ke kotun zaben.

Kara karanta wannan

Sanatan APC: Atiku da Obi na bata lokaci a kotu, babu mai tsige Tinubu a mulki

Kazalika, sauran wadanda aka yi kara, kamar Shugaba Tinubu da APC, ba su nuna kin yarda da gabatar da takardun a matsayin hujja ba.

PDP Da Atiku Sun Gabatar Da Rahoton EU a Matsayin Hujja

Amma, jagoran lauyoyin da ke kare Atiku, Chris Uche, ya nuna kin amincewa yana mai kira ga kotun kada ta karbi hujjar.

Yayin yi wa shaidan tambayoyi, jagoran lauyoyin PDP, Chris Uche, ta gabatar da rahoton tawagar masu saka ido kan zabe na Tarayyar Turai, EU, a matsayin hujja kan Shugaba Tinubu.

Wadanda ake kararsu (Tinubu, INEC, da APC) duk sun nuna rashin amincewa da rahoton suna kira ga kotun ta yi watsi da shi. Amma, kotun ta karbi rahoton na EU ta bukaci wadanda aka yi karar su shirya kare kansu.

Kotu Ta Dage Sauraron Karar Atiku Kan Zaben Shugaban Kasa

Tunda farko mun kawo muku cewa kotun sauraron karar zaben shugaban kasa ta dage cigaba da sauraron karar jam'iyyar PDP da Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasarta a zaben 2023.

Kara karanta wannan

Ahir dinku: Tinubu ya dagawa Turawa EU yatsa kan rahoton zaben 2023, ya caccake su

Vangaurd ta rahoto cewa kotun mai alkalai biyar karkashin jagorancin Mai Shari'a Haruna Tsammani ta dage cigaba da sauraron karar ne zuwa 18 ga watan Mayu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164