Majalisa ta 10: Kwamitin Ayyuka Na PDP Ya Zargi APC Da Shiga Sha'aninta Kan Kujerar Shugaban Marasa Rinjaye

Majalisa ta 10: Kwamitin Ayyuka Na PDP Ya Zargi APC Da Shiga Sha'aninta Kan Kujerar Shugaban Marasa Rinjaye

  • Kwamitin ayyuka na kasa (NWC), na jam’iyyar PDP, ya zargi jam’iyya mai mulki (APC) da yunkurin shirya zagon kasa dangane da kujerar shugaban marasa rinjaye na Majalisar Dattawa ta 10
  • Kwamitin ya ce jam’iyyar PDP na ganawa da mambobinta na Majalisar Dattawan don yanke shawara kan wadanda za su tsaida
  • Mai magana da yawun jam’iyyar PDP na kasa, Debo Ologunagbe, ya ce da zarar sun kammala tattaunawa, za su tura sunayen wadanda suka zaba zuwa ga shugaban majalisar

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Kwamitin ayyuka na jam’iyyar PDP na kasa (NWC), ya zargi jam’iyyar APC mai mulki da yunkurin kawo rudani a zaben shugaban marasa rinjaye na Majalisar Dattawa ta 10.

Mai Magana da yawun jam’iyyar PDP na kasa, Debo Ologunagba ne ya yi zargin a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, kamar yadda ya zo a rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Jam’iyyar APC Ta Fitar da Sanatoci, ‘Yan Majalisa da Za a Warewa Sauran Mukamai 8

PDP ta zargi APC da kulla mata makarkashiya a Majalisar Dattawa
PDP ta zargi APC da shirya wata kulalliya dangane da kujerar shugaban marasa rinjaye na Majalisar Dattawa. Hoto: @OfficialPDPNig
Asali: Twitter

PDP ta zargi APC da shirya makarkashiya game da kujerar shugaban marasa rinjaye na majalisa

Ologunagba ya zargi jam’iyyar APC da yunkurin kulla wata makarkashiyar da za ta dagula zaben shugaban marasa rinjayen da za a gudanar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mai magana da yawun jam’iyyar ta PDP ya ce har yanzu ba su gama tattauanawa ba dangane da wanda za su tsada neman kujerar marasa rinjayen na Majalisar Dattawa ta 10.

Ya kara da cewa daga cikin shirin da suke yi gabanin zaben, kwamitin ayyuka na PDP ya gana da duka sanatocin PDP na majalisar.

PDP ta ce ta fadawa sanatocinta abinda ya dace su yi

Ya bayyana cewa sun tattauna muhimmancin samun tsayayyar hamayya a cikin majalisar kasa da sanatocin, wadanda suka bas u tabbacin cewa za su kare dimokuradiyyar Najeriya, kamar yadda The Cable ta kawo.

Kara karanta wannan

Rikici: Babbar Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Matakin Korar Tsohon Gwamna Daga Cikin Jam'iyyar PDP

Ya kuma ce an dorawa kwamitin ayyukan na PDP alhakin sanar shugaban Majalisar Dattawan, Godswill Akpabio cewa har yanzu ba su gama yanke shawara ba game da wanda za su sanya a kujerar shugaban marasa rinjaye na majalisar.

Ologunagba ya kara da cewa, da zarar an kammala zabar wadanda aka amince da su, za a mika sunayensu ga shugaban Majalisar Dattawan don yin abinda ya dace.

Ya kuma ce jam’iyyar ta yabawa ‘yan Majalisar Dattawan bisa hadin kai, dagewa, aminci da jajircewarsu wajen ciyar da dimokuradiyyar Najeriya gaba.

Kungiyar PDP ta ki amincewa da Tambuwal a matsayin shugaban marasa rinjaye na Majalisar Dattawa

Legit.ng a baya ta kawo muku rahoto kan wata kungiya ta jam’iyyar PDP, da ta ki amicewa da zabin tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, a matsayin shugaban marasa rinjaye na Majalisar Dattawa ta 10.

Kungiyar ta ce bai kamata jam’iyyar ta PDP ta amince da Tambuwal ba duba da irin abinda ya yi a baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng