Majalisa Ta 10: An Haramtawa 'Yan Jaridu Shiga Zaman Majalisar, Ba A Bayyana Dalilin Ba

Majalisa Ta 10: An Haramtawa 'Yan Jaridu Shiga Zaman Majalisar, Ba A Bayyana Dalilin Ba

  • Jami'an 'yan sanda sun hana 'yan jarida shiga majalisar dattawa yayin zamansu a yau Talata
  • Wani dan sanda ya tare bakin kofar majalisar inda ya ce babu wani mahaluki da zai shiga ciki
  • Kungiyar 'yan jaridu ta yi Allah wadai da wannan mataki inda ta ce hakan ya sabawa dokar kasa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - An samu rudani yayin da aka hana 'yan jarida shiga cikin zaman majalisar dattawa a Abuja.

Sajan din dan sanda mai kula da majalisar shi ya hana 'yan jaridan shiga majalisar ba tare da bayyana wani dalili ba.

Majalisa ta 10: 'Yan sanda sun hana 'yan jaridu shiga zaman majalisa
Majalisar Dattawa A Najeriya. Hoto: National Assembly.
Asali: Twitter

Sai dai ba a ba da wani dalili ba na daukar wannan mataki, The Cable ta tattaro.

Duk wata hanya da take nuna zaman majalisar kai tsaye kamar ta manhajar Twitter da sauran kafafen intanet suma ba sa aiki.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Sweden: Ba Da Yawunmu Aka Kona Kur'ani Ba, Muna Tir Da Hakan

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Dan sanda ya hana 'yan jarida shiga majalisar

Daya daga cikinsu mai suna Dengi ya jaddada cewa ba zai taba barin wani dan jarida ya shiga cikin majalisar ba, bare ya nadi wani abu.

Kokarin fahimtar da shi amfanin shigan 'yan jaridun cikin majalisar yaci tura yayin da danna wa kofar kwado ya wuce, cewar rahotanni.

Wannan mataki da majalisar ta dauka ta sabawa dokar 'yancin samun bayanai da ta ba wa dan kasa da kuma 'yan jaridu damar nadar bayanai.

Kungiyar 'yan jaridu ta gargadi majalisar kan wannan mataki

Kungiyar 'Yan Jaridu (NUJ) ta fitar da wata sanarwa inda ta bukaci majalisar ta janye wannan mataki da ta dauka.

Ta ce 'yan jaridu suna da 'yancin nadar bayanai musamman daga hukumomin gwamnati, inda ta bukaci majalisar ta yi bincike don gano dalilin yin hakan.

Kara karanta wannan

'Rashin Da'a Ga Buhari': Tajudeen Abbas Ya Barranta Kansa Da Kalaman Hadiminsa

Hukumar SERAP a na ta bangaren ta yi barazanar maka majalisar a kotu idan ba ta janye wannan mataki ba da kuma ba da hakuri kan tauye musu hakki.

Hukumar ta ce wannan mataki na majalisar ya sabawa dokar 'yancin dan Adam na damar samun bayanai.

Akpabio Ya Nemi Bukatu Guda 2 Wurin Tinubu Bayan Zama Shugaban Majalisar

A wani labarin, sabon shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya nemi wasu bukatu a wurin Shugaba Tinubu.

Akpabio ya nemi wadannan bukatu ne yayin gabatar da jawabin godiya bayan samun nasara.

Ya bukaci shugaban kasa ya rika tura kasafin kudi akan lokaci da kuma tabbatar da akwai kudin a kasa kafin a tura.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.