Jiga-Jigan APC Sun Yi wa Juna Jina-Jina Saboda Neman Mukami a Gwamnatin Tinubu
- Bangarorin jam’iyyar APC sun barke da rikice-rikicen cikin gida musamman bayan zaben 2023
- Kowane bangare ya na zargin abokin fadansa da cin amanar APC da yi wa ‘yan takaranta zagon-kasa
- Wannan rigima ce ta ke neman cin Ovie Omo-Agege wanda ya yi wa APC takarar Gwamna a Delta
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Abuja - Jam’iyyar APC ta reshen jihar Delta ta samu kan ta cikin rikicin gida a sakamakon manyan zabukan da aka shirya a Fabrairu da Maris.
Wani dogon rahoto da aka samu daga Daily Trust ya nuna duk da irin nasarorin da jam’iyyar ta samu a zaben majalisa, rigingimu sun dabaibaye APC.
A sakamakon rikicin ne aka kori tsohon Darektan kwangiloli na NDDC, Cairo Ojougboh daga APC, Hilary Fada Ibude ya yanke wannan hukunci.
Omo-Agege vs Cairo Ojougboh
A matsayinsa na shugaban jam’iyya na reshen Ika ta Kudu, Hilary Fada Ibude ya zargi tsohon ‘dan majalisar da goyon bayan jam’iyyar LP a zaben 2023.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ojougboh ya ce Sanata Ovie Omo-Agege ne kurum yake yi masa bita-da-kulli. A gefe guda, ana zargin ‘dan takaran Gwamnan da cin amanar Bola Tinubu.
Ana haka ne sai aka ji ‘yan bangaren Ulebor Isaac na jam’iyyar APC a yankin Ughelli sun dakatar da Omo-Agege wanda shi ya yi masu takarar Gwamna.
Ba a dade ba sai Omeni Sobotie ya soke dakatarwar da aka yi tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan, ya na mai kaca-kaca da su Ulebor Isaac.
Ana rigima tun bayan zaben 2023
Kafin nan rahoto ya zo cewa shugabannin mazabar Onicha-Olona a Aniocha ta Arewa sun zargi Lauretta Onochie da zagon-kasa, APC ta fatattake ta.
Rigingimun na APC bai tsaya a nan ba, ya shafi shari’ar korafin zabe da aka yi a garin Asaba. Wasu su na ganin lamarin ya koma neman fada ne a Abuja.
Rikicin Elder Sobotie da Michael Inana
An rahoto Sakataren yada labaran APC na Delta, Valentine Onojeghuo ya na cewa masu adawa da Omo Agege wasu ‘yan PDP ne a rigar jam’iyyarsu.
Valentine Onojeghuo yake cewa Michael Inana da mutanensa su na neman fada ne a wajen Bola Tinubu, saboda ya ba su mukamai a gwamnatin tarayya.
Neman rikon kwamiti a majalisa
Kusan babu sabo ko tsohon ‘dan majalisar tarayya wajen neman samun kwamiti mai maiko, mun ji labari ‘Yan APC, PDP, LP da NNPP, YPP su na tsere.
Akwai wadanda sai da aka yi yarjejeniya da su kafin su goyi bayan takarar Rt. Hon. Tajuddeen Abbas, a yau majalisa za ta dawo aiki bayan hutun idi.
Asali: Legit.ng